✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Yan sanda sun saki Nastura Ashir

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta sako jagoran Gamayyar Kungiyoyin Arewacin Najeriya (CNG), Nastura Ashir Sheriff. ‘Yan sanda sun kama shi ne bayan ya jagoranci zanga-zangar…

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta sako jagoran Gamayyar Kungiyoyin Arewacin Najeriya (CNG), Nastura Ashir Sheriff.

‘Yan sanda sun kama shi ne bayan ya jagoranci zanga-zangar rashin tsaro da ke addabar Arewacin Najeriya da aka gudanar a Katisna.

Majiyarmu ta shaida mana cewa an saki Nastura Ashir ba tare da a gindaya masa wani sharadi ba kuma ‘yan sandan ba su bayyana wane laifi ake tuhumarsa da aikatawa ba.

Shugaban Kungiyar Matasan Arewa ta AYCF Yarima Shattima ya sanya hoton da suka dauka da IG Wala tare da Nastura a daidai lokacin da yan sanda suka sako shi, a shafin sa na sada zumunta.

Ya sanya hoton a Facebook ya ce, “Nastura ya sami ‘yanci, gani tare da shi a harabar hedikwatar rundunar ‘yan sanda a Abuja”, inji shi.

Kame Nastura da ‘yan sanda suka yi ya sanya wasu fitattun mutane a Arewaci da Kudancin kasar sanya baki a maganar inda suka nemi a sake shi.