✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan sanda sun kashe dan bindiga a Edo

An yi dauki-ba-dadi tsakanin ’yan sanda da ’yan ta’addan

Rundunar ’Yan sanda a Jihar Edo ta sanar da samun nasarar kashe wani dan ta’adda da ake zargin yana daga cikin masu garkuwa da mutane a jihar.   

Bayanan rundunan sun nuna cewa, jami’an rundunar sun sheke wanda ake zargin ne a ranar Litinin a kan Babbar Hanyar Benin zuwa Legas kusa da kauyen Utekon, bayan musayar wutar da aka yi tsakanin ‘yan sanda da gungun ‘yan ta’adda.

Mai magana da yawun rundunar, SP Chidi Nwabuzor ne ya tabbatar da hakan yayin zantawarsa da manema labarai a Benin, babban birnin jihar.

Nwabuzor ya ce jami’ansu sun bazama aiki ne biyo bayan kiran da suka samu game da wani gungun ’yan ta’adda da suka tare Babbar Hanyar Benin-Legas, kusa da kauyen Utekon.

Ya kara da cewa, ganin ’yan sandan ke da wuya sai ’yan ta’addan suka bude musu wuta, lamarin da ya sanya su ma jami’an suka mayar da martani.

Ya ce bayan dauki-ba-dadin da aka yi tsakanin bangarorin biyu, a karshe ’yan sanda sun bindige mutum daya sannan sauran sun tsere dauke da bindigoginsu.

Jami’in ya ce za su ci gaba da bincike domin kamo ragowar ’yan ta’addan da suka ranta a na-kare.

(NAN)