✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Yan sanda sun gano gawarwakin mutum 10 a dajin Edo

'Yan sanda sun gaza gano musabbabin mutuwarsu.

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Edo, ta ce jami’anta sun gano gawarwaki maza 10 wadanda shekarunsu ya kai tsakanin 23 zuwa 25 a cikin dajin Ibillo-Lampese a kan hanyar Legas zuwa Abuja. 

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin rundunar a jihar, SP Chidi Nwabutor, ya fitar ranar Laraba a Benin, babban birnin jihar.

Nwabutor ya bayyana cewa, ta hanyar sahihan bayanan sirri, jami’an rundunar tare da hadin gwiwar ‘yan banga da mafarauta ne suka gano gawarwakin ranar Talata da misalin karfe 11:00 na safe.

Ya ce rundunar ta gano gawarwakin wanda maza ne guda 10 da suka mutu masu shekaru 23 zuwa 25.

“A yayin binciken farko, an dauki hotunan gawarwakin.

“Har ila yau, an bincika gawarwakin amma babu wata alama ta tashin hankali ko kayan da za su kai ga gano inda suka fito.

“Al’ummar yankin sun bayyana cewa gawarwakin ba ’yan kabilarsu ba ne.

“Tuni aka killace gawarwakin a babban dakin ajiye gawa na asibitin Ibillo don gudanar da binciken kwakwaf,” in ji Nwabutor.

Ya ce kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Mohammed Dankwara, ya roki jama’a da su bayar da bayanai masu inganci da za su kai ga gano musabbabin mutuwar matasan.

Ya ce irin wadannan bayanai na iya sa a kama duk wanda yake da hannu a kisan nasu.