✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan sanda sun bindige ’yan bindiga a Neja

’Yan bindiga uku sun sheka lahira a wata arangama da suka kwashi kashinsu a hannun ’yan sanda a Jihar Neja. Rundunar ’Yan Sandan Jihar ta…

’Yan bindiga uku sun sheka lahira a wata arangama da suka kwashi kashinsu a hannun ’yan sanda a Jihar Neja.

Rundunar ’Yan Sandan Jihar ta ce an yi musayar wuta da masu garkuwa da mutanen ne a Karamar Hukumar Lapai inda aka yi garkuwa da mutane uku a wurare daban-daban.

Kakakin Rundunar, DSP Wasiu Abiodun ya ce bayan samun labarin ne jami’an ’yan sanda da hadin gwiwar ’yan banga a Lapai suka bi sawun bata-garin zuwa cikin daji, kusa da kauyen Fapo inda aka yi dauki-ba-dadi.

“A nan aka bindige uku daga cikinsu, aka kwato bindiga kirar AK47 guda uku, sauran masu garkuwar suka tsere, aka kuma ceto mutum ukun da aka sace,” inji shi.

Ya ambato Kwamishinin ’Yan Sandan Jihar, Adamu Usman, na kira ga jama’ar Jihar su kwantar da hankalinsu, su ci gaba da harkokinsu yadda suka saba.

Sannan ya roke su da su taimaka wa Rundunar da rahoton duk wanda aka gani da raunin harbi.