✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan sanda 3 sun mutu a hatsarin mota a Kaduna

Daya daga cikin tayoyin motar ‘yan sanda ce ta fashe a kauyen Sako.

Wasu ’yan sanda uku sun rasa rayukansu a wani hatsarin mota da ya rutsa da su a garin Kidanda da ke Karamar Hukumar Giwa a Jihar Kaduna.

’Yan sandan na tafiya ne zuwa Karamar Hukumar Giwa bayan halartar bikin Hawan Daushe a birnin Zariya a ranar Lahadi, inda hatsarin ya afku da misalin karfe 9 na dare.

Wakilinmu ya ruwaito cewa daya daga cikin tayoyin motar ‘yan sanda ce ta fashe a kauyen Sako, a Kidanda, wanda kuma ya yi sanadiyar mutuwar jami’an guda uku.

Wasu uku kuma sun jikkata, inda aka garzaya da su asibiti domin kula da lafiyarsu a cewar majiyoyi.

Hotunan da aka gani, sun nuna jami’an jina-jina, inda wasu suka samu munanan raunuka a kawunansu.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ’yan sandan jihar, DSP Mohammed Jalige, ya tabbatar da faruwar hatsarin tare da yi wa jami’an da suka rasu addu’a da kuma fatan samun sauki ga wadanda suka jikkata.