✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan Najeriya da suka je Umara sun makale saboda rikicin Sudan

Yawancin wadanda abin ya shafa sun tafi Umara ne daga Kano a jiragen kasar Sudan

Daruruwan ’yan Najeriya da suka tafi Umara kasar Saudiyya sun makale sun kasa dawowa a sakamakon yakin kasar Sudan.

Masu Umarar sun makale a Kasa Mai Tsarki ne sakamakon rufe harkokin jiragen sama a Sudan, inda jiragen da da suka bi suka fito.

Tsohon Shugaban Kamfanonin Jigilar Aikin Hajji da Umara ta Najeriya (AHUON) Alhaji Abdulfatah Abdulmojeed, ya shaida mana cewa yawancin wadanda abin ya shafa sun tafi Umara ne daga Kano a jiragen kasar Sudan.

Aminiya ta gano cewa wadanda wannan matsalar ta shafa fasinjojin kamfanin jiragen sama na Badr Air na kasar Sudan ne.

Kamfanin Badr Airline dai ya rufe harkokinsa a sakamakon tsanantan rikicin da ya yi sanadin harbo wasu jiragensa guda biyu a birnin Khartoum a makon jiya.

Duk da haka ana dawowa Najeriya

Sai dai duk da haka, ’yan Najeriya da suka tafi Umara ta kamfanonin jirage irin su Qatar Airways da Egypt Air da sauransu suna ci gaba da dawowa gida.

Amma sukan kauce wa bi ta sararin samaniyar kasar Sudan, wadda yaki ya sa aka rufe, wanda kuma ke kara wa tafiyar tasu tsawo.

Kauce wa sararin samaniyar Sudan mai fama da yaki ne ya sa a lokacin da Shugaba Buhari ya kai ziyarar aiki da Umara a kasar Saudiyya ya shafe awa bakwai a hanyarsa ta dawowa Najeriya, maimakon awa hudu da rabi zuwa Abuja.

Jiragen da ke zuwa Saudiyya daga Najeriya sukan fita kasar ne ta Maiduguri, su bi ta Chadi, sannan su shiga Sudan kafin su shiga Jidda na kasar Saudiyya.

Halin da fasinjoji ke ciki

Duk da cewa jiragen wasu kamfanoni sukan kauce wa Sudan saboda dalilan tsaro, amma Badr Air ya dakatar da harkokinsa, abin da ya jefa fasinjojin kamfanin da ke neman dawowa bayan kammala Umara cikin tsaka mai wuya.  

Wani fasinjan kamfanin ya shaida mana cewa “Yanzu ina Saudiyya, kamfanin ya ce in nemi mafita. Zabin da muka samu shi ne na biyo jirgin FlyNas a kan Naira dubu 550, idan yakin ya lafa Badr Air zai dawo mana da N350,000.

“Yanzu ejen-ejen na kokarin nema wa fasinjojinsu mafita, ga shi kudin masaukin da muka biya ya kare, mun kosa mu koma gida.

“Sai da ta kai ga masu otel sun kashe mana ruwa da wutar lantarki na kusan kwana biyu sai da muka yi musu bore.” 

Aminiya ta gano cewa su kansu wadanda suka bi jiragen da ke kauce wa Sudan kudinsu na dawowa ya karu.

Amma wata majiya daga wani kamfanin jirage ta shaida mana cewa, “Amma idan kudin tafiya da dawowa ka biya, to ba za ka samu kari ba, kamfanin jirgin da ka biya ta shafa.

Wani mamba a kungiyar AHUON ya tabbatar mana cewa ejen-ejen din kamfanonin jirage da dama suna Saudiyya inda suke kokarin sama wa fasinjojinsu mafita domin dawo da su gida.