✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan Kasuwar Sabon Gari sun maka Ganduje a Kotu

’Yan Kasuwar na zargin gwamnan da tashinsu da karfin tsiya daga shagunansu

’Yan tireda a Kusawar Muhammadu Abubarkar Rimi da ke Sabon Gari Kano sun maka Gwamna Abdullahi Ganduje a kotu saboda neman tashinsu daga shagunansu.

Gwamnatin Jihar Kano ta ba wa ’yan kasuwar wa’adin tashi daga shagunan nasu ne bisa zarginsu da rashin gaskiya da saba alkawari.

Kamfanin gwamnatin jihar da ke gudanar da kasuwar ya yi karar ’yan tiredar ne a kotun Mai Shari’a Muntari Dandago yana neman ta umarce su su tashi daga shaguban gwamanti.

Su kuma sun kalubalanci karar da cewa yunkurin tashin su da karfin tsiya ne kuma kotun da ke zamanta a titin Airport Road ba ta da hurumin saurarar karar.

A yayin zaman kotun na ranar Alhamis, lauyan ’yan kasuwar, Abdul Azeez ya ce ci gaba da sauraron karar saba tsarin aikin kotu ne saboda Babbar Kotun Jiha ta riga ta fara sauraron sharia’ar.

Barista Azeez ya ce ’yan kasuwar sun riga sun shigar da kara a gaban Babbar Kotun Jihar suna kalubalantar yunkurin gwamnatin jihar na tilasta musu amfani da wutar lantarki mai amfani da hasken rana a kasuwar.

Mai Shari’a Muntari Dandago ya dage ci gada da sauraron shari’ar zuwa ranar 16 ga watan Disamba, 2020.