✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan kasuwa 2 sun yi kashin kunshi 193 na Hodar Iblis a hannun NDLEA

Daya daga cikinsu ya yi kashin kunshi 100 na Hodar Iblis wanda nauyinta ya kai kilo 2.137.

Wasu ’yan kasuwa biyu sun yi kashin kunshi 193 na Hodar Iblis bayan shafe kwanaki uku a hannun jami’an Hukumar Yaki da Fataucin Miyagun Kwayoyi (NDLEA).

Bayanai sun ce an cafke ababen zargin biyu ne a Filin Jirgin Sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja, a ranar 10 ga watan Mayu yayin shigowarsu Najeriya daga kasar Uganda.

Mai Magana da Yawun NDLEA, Femi Babafemi ne ya tabbatar da hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a wannan Lahadin.

Mista Babafemi ya ce an dade ana neman mutanen biyu ruwa a jallo wadanda ake zargi ba su da wata sana’a face safarar miyagun kwayoyi.

Ya bayyana cewa bayan shafe kwanaki a hannun hukumar, daya daga cikinsu ya yi kashin kunshi 100 na Hodar Iblis wanda nauyinta ya kai kilo 2.137, yayin da abokin tafiyarsa ya yi kashin kunshi 93 na hodar mai nauyin kilo 1.986.

Kazalika, jami’an NDLEA sun kai samame wata mashayar miyagun kwayoyi a titin Bama da ke Sabon Gari da kuma Filin Wasa na Sani Abacha da ke birnin Kano, inda suka cafke ababen zargi 160 dauke da miyagun kwayoyi daban daban-daban.

Haka kuma, hukumar ta cafke wasu mutum biyu a titin Kano zuwa Maiduguri da tarin miyagun kwayoyi da suka hada da kwayoyi 5,000 na tramadol.

Wannan na zuwa ne a yayin da jami’an hukumar suka cafke wasu ababen zargi 25 a yankunan Tora Bora, Gwarinpa, Karmo, Kasuwar Garko, Bwari da sansanin ’yan gudun hijira na Kucigoro da ke Abuja.