✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan fashi sun harbi masu neman sabbin kudi a shagon POS

’Yan fashin sun yi awon gaba da makudan kudade bayan sun harbi mai shagon POS da kwastomominsa

Wasu mahara sun kai hari a wani shagon POS da tsakar rana, suka harbi mai shagon da kwastomominsa, sannan suka yi awon gaba da makudan kudade a Jihar Bauchi.

Ana zargin ’yan fashin sun yi awon gaba da akalla Naira miliyan bakwai, kuma sun kai harin ne da nufin satar sabbin takardun kudi.

“Wadanda harin ya shafa sun je neman sabbin kudi ne a shagon, ana cikin haka ne ’yan fashi suka far musu suka bude masu wuta,” in ji Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Bauchi, Aminu Alhassan.

Wannan mummunan lamari dai ya faru ne wata tashar mota a ranar Litinin kamar yadda hukumar ’yan sandan jihar ta tabbatar.

Da yake jawabi a Fadar Galadiman Katagum, Usman Mahmood Abdullahi, kwamishinan ’yan sandan jihar, ya ce an auna arziki ba a samu asarar rai ba a harin.

Amma ya ce duk da haka, “Da yardar Allah, za mu ci gaba da yin bakin kokarinmu wajen cafke wadanda suka yi wannan danyen aiki, duk da cewa yanzu sun tsere.”

Abin da Gwamna ya ce

A yayin ziyarar jaje da ya kai Fadar Sarkin Katagum, Dokta Umar Faruk II, kan aukuwar lamarin, Gwmanan Jihar Bauchi, Bala Mohammed ya bukaci kwamishinan ’yan sandan da a kara adadin jami’an tsaro a yankin Zaki don hana maimaituwar hakan.

Gwamnan, wanda ya samu rakiyar shugabannin tsaro da manyan jami’an gwamnatinsa ya kuma ziyarci wadanda abin ya shafa da kuma wurin da aka kai harin.

Ya ce lamarin ya haifar da zullumi ga mazauna yankin Zaki, wanda ke kan hanyar zuwa jihohin Yobe, Jigawa da kuma Kano.