✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan canji na taimaka wa ’yan ta’adda wajen shigo da makamai – Emefiele

Ya yi zargin kaso mai tsoka na Dalar na tafiya ne wajen shigo da makamai kasar nan.

Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele ya ce sun bankado yadda ’yan ta’adda ke sayen Dalar Amurka daga hannun masu canjin kudaden waje domin shigo da makamai.

Ya yi zargin cewa kaso mai tsoka na Dalar da ’yan canji ke saye tana tafiya ne wajen shigo da makamai kasar nan ba bisa ka’ida ba.

Ya bayyana hakan ne ranar Juma’a yayin da yake jawabi ga ’yan jarida a karshen taron tattaunawa kan hada-hadar kudi na watan Satumba na babban bankin.

Gwamnan, ya kuma sha alwashin cewa bankin sai ya ga bayan dukkan masu samun Dalar ta haramtattun hanyoyi.

“Ko Boko Haram, ko garkuwa da mutane ko ma kowanne irin nau’i na ta’addanci ake yi a kasar nan, ’yan canji ne suke daukar Dala su sayar wa da irin wadannan mutanen, su kuma su je su sayo makamai su zo su cutar da mu.

“Abin da mutane suke so fa mu ci gaba da yi kenan. Hakan ba zai yuwu ba. Ba zamu iya ba. Idan kana da kowanne irin halastaccen kasuwanci, ka je banki ka nuna musu, za su sayar maka da Dala.

“Idan ma har sayayyar da zaka yi ta haura ka’idar yawan kudin da muka saka, sannan muka gano kana da bukatar kari na gaskiya, bankinka zai iya yi mana magana mu kuma kara maka,” inji Gwamnan na CBN.

Ya shawarci daidaikun jama’a da ma kamfanoni da ke da bukatar Dalar da su rika zuwa bankuna kai tsaye.

Emefiele ya kuma sha alwashin cewa bankin zai ci gaba da yin dirar mikiya a kan masu samun Dalar ta haramtattun hanyoyi.

“Za mu kama masu zuwa su yi takardar fita waje da sauran takardu na bogi saboda kawai su yaudari bankuna a basu Dala su kuma je su sayar da tsada ta hanyar yin amfani da EFCC da sauran hukumomin yaki da cin hanci,” inji Gwamnan.