✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun yi garkuwa da uwa da danta a Abuja

Wasu ’yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun yi garkuwa da da wata matar aure mai suna Blessing Alex tare da…

Wasu ’yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun yi garkuwa da da wata matar aure mai suna Blessing Alex tare da danta da wasu mutum biyu.

An dai yi garkuwa da Blessing tare da danta mai suna Frank Alex mai shekara 18 da wasu mutunen biyu ne a unguwar Ukya Tsoho da ke karamar Kuje a Yankin  Babban Birnin Tarayya.

Sauran mutum biyu da aka yi garkuwan da su su ne Saidu Ibrahim da Zabe Alkali.

Mijin matar, Johnny Alex, ya ce an yi garkuwa da maidakinsa Blessing ne a daren Juma’a da misalin karfe 8:12, lokacin da ’yan bindigar suka kai hari cikin unguwar suka yi ta harbi.

“Madakina tana dakin dafa abinci tana girka miyar abincin sayarwa, a wannan lokacin ’yan bindigar suka yi dirar mikiya tare da zagaye gidan,” in ji Mista Alex.

Mista Alex ya kara da cewa, “Ina cikin shagon sayar da abinci tare da dana masu saye sun zo, sai na ji karar bindiga; nan take na sanar da maidakina da ta gudu ta boye. Kafin ta tsere sun kama ta tare da danmu sun yi awon gaba da su.”

Daga nan ’yan bindigar suka shiga shagon suka kwashe lemon kwalda da taliya da biskit da buhun shinkafa da wake da man ja da wasu kayan girki.

Sauran mutum biyun kuwa sun shigo shagon ne da niyyar cajin wayar salula sai ‘yan bindigar suka hada da su.

Masu garkuwa da mutanen dai sun kwashe akalla wayoyin salula 25 a shagon.

Mista Alex ya ce “ranar Asabar ’yan bindigar suka kira waya sannan suka bukaci a biya kudin fansa Naira miliyan 10 kafin su sako maidakina da da na,  a ina zan samu wannan kudin?”