✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun yi garkuwa da ‘manoma’ 60 a Sakkwato

An sace su ne bayan sun fita gonakinsu aiki

’Yan bindiga sun yi garkuwa da mutum 60 bayan sun tafi gonakinsu aiki a kauyukan da ke Karamar Hukumar Sabon Birni ta Jihar Sakkwato.

Rahotanni sun ce an yi garkuwa da mutanen ne cikin kwana biyu a kauyukan Katuma da Dan Aduwa da Unguwar Lalle da Marna da Tsamaye dukkansu a Karamar Hukumar.

Wata Majiya a a yankin ta shaida wa Aminiya cewa ’yan bindigar da yawansu bai kai 20 ba, sun shiga kauyukkan ne da safiyar Lahadi suka tafi da mutum 40 bayan sun fita gona domin aikin damina.

Daga nan ne kuma suka sake dawowa a Litinin suka tafi da mutane 20 domin sun fita aikin gona ba da izininsu ba.

Majiyar ta ce ’yan bindigar sun sake tare hanyar Kwanar Maharba da ta hada garin Sabon Birni da Sakkwato inda suka hana shiga ko fita a yankin.

“A kauyen Dan Gawo an harbe mutum tara, biyu sun mutum shida na kwance a babbar asibitin Sabon Birni, kafin su yi garkuwa da mutanen ne suka yi haka, lamarin nan barazanar tsaro ya dawo mana a yankinmu,” a cewar majiyar.

Honarabul Aminu Almustafa wanda aka fi sani da Boza da ke wakiltar Sabon Birni ta yamma a Majalisar Dokokin Jihar ya ce ’yan bindigar suna addabarsu, inda ko a wannan Litinin suka tafi da mutum 81 don kawai sun tafi gona.

“Bayan ’yan bindigar sun shigo kauyukanmu mun kira jami’an tsaro domin su ba mu dauki har yanzu da muke magana da kai ba wanda ya zo wajenmu a cikinsu, ya kamata gwamnati ta taimaka mana a yankinmu musamman a wannan lokacin da muke ciki na damina,” a cewar Aminu Boza.

Ya ce maharan sun harbe mutum tara, biyu sun rasu, yayin da sauran ke kwance asibiti.

Duk yunkurin wakilinmu na jin ta bakin jami’in huldar da jama’a na Rundunar ’Yan Sandan jihar, DSP Sanusi Abubakar ya ci tura har zuwa lokacin hada wannan rahoton.