✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun yi garkuwa da ’yan kasuwa a hanyar Birnin Gwari

Wani mai gari a ya ce ’yan kasuwa sama da 70 ne a ayarin motoci 20 tare da rakiyar ’yan sanda.

’Yan bindiga sun yi garkuwa da ’yan kasuwa matafiya da ba san adadinsu ba a Babbar Hanyar Birini Gwari  zuwa Kaduna a ranar Laraba.

Kawo yanzu dai babu cikakken bayani game da abin da ya faru, amma majiyarmu ta ce yawancin mutanen da lamarin ya ritsa da su ’yan kasuwa ne da ke kan hanyarsu ta zuwa Kano.

Wani basarake a yankin, Muhammad Umaru, ya shaida wa Aminiya cewa, “Daga garin Udawa kadai akwai ’yan kasuwa sama da 70 ne ke cikin ayarin.

“Akwai kuma wasu ’yan kasuwa daga kauyukan da ke makwabtaka da mu da ke cikin ayarin da aka tare; Har da makwabatana a ciki, mun kira wayoyinsu amma ’yan bindiga ne suka amsa.”

Malam Muhammad ya bayyana cewa motoci sama da 20 dauke da ’yan kasuwar ne suka yi ayari tare da rakiyar ’yan sanda, amma ’yan bindigar suka tare su.

Wata majiyarmu ta bayyana cewa wasu daga cikin matafiyan da suka samu tserewa zuwa cikin daji ne suka kira ’yan uwansu daga baya suka sanar da su abin da ya faru.

Kakakin ’yan sandan jihar Kaduna, ASP Jalige Mohammed, bayan wakilinmu ya tuntube shi ya shaida masa cewa zai waiwaiye shi idan ya samu karin bayani.

Babu tuba ga ’yan bindiga —El-Rufai

Harin na zuwa ne kasa da awa 24 bayan Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya ce gwamnatin jihar ba za ta taba karbar tubar ’yan bindiga ba.

El-Rufai ya ce gwamnatin jiharsa ba ta yarda ba tubar ’yan ta’adda ba kuma ba ta da niyyar karbar tubar duk wani dan bindiga.

Ya ce, “Babu wani wanda za a so a ce mana tubabben dan ta’adda ne. A wurinmu, dan bindigar da aka kashe kawai shi ne tubabbe. Abin da muke so kawai shi ne mu kashe su, su je lahira su hadu da Allah,” inji gwamnan.

Ya bayyana haka ne a Fadar Shugaban kasa inda ya gana da Shugaba Muhammadu Buhari bayan harin da ’yan bindiga suka kashe mutum 40 a Karamar Hukumar Giwa ta jiharsa.

El-Rufai tare da Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gidan jihar, Samuel Aruwan, ya ce ayyana ’yan bindiga da kotu ta yi a matsayin ’yan ta’adda ya ba wa sojoji karin karfin ragargazar su babu kakkautawa.

Saboda haka ya bukaci sojojin da kada su raga wa duk wani dan bindiga a Jihar Kaduna.

A cewarsa, sojoji na sane da inda ’yan bindigar suke boye, amma ya yi karin haske cewa jami’an tsaro suna taka-tsantsan ne domin guje wa kashe fararen hula a kokarin hallaka bata-garin.

Ya roki Gwamnatin Tarayya ta tura karin jami’an tsaro, sannan ta kara daukar sabbin ’yan sanda da sojoji saboda karancinsu ba zai ba su damar gudanar da aikinsu cikin nasarar da ake bukata ba.