✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan bindiga sun sace mutum 5 a Tegina

Ko a farkon shekarar nan sai da suka sace wasu daliban Islamiyyah a garin.

Akalla mutum biyar ne rahotanni suka tabbatar da sace su bayan wani harin ’yan bindiga a garin Tegina da ke Karamar Hukumar Rafi ta Jihar Neja.

Ko a farkon wannan shekarar sai da maharan suka sace wasu daliban makarantar Islamiyyah a garin.

Majiyoyi a yankin sun shaida wa Aminiya cewa ’yan bindigar sun sake dawowa yankin a karshen makon da ya gabata inda suka yi awon gaba da wasu ma’aikatan masana’anta su biyar.

Maharan dai wadanda yawansu ya kai mutum 10 an ce suna dauke da bindigun AK-47 ne a yayin harin.

Sun kai hari garin ne da misalin karfe 9:00 na daren ranar Asabar, sannan suka wuce kai tsaye zuwa wani gidan sarrafa ruwan leda da ke daura da wata makarantar sakandaren ’yan mata ta garin.

“Sun shammace mu matuka saboda a kafa suka shigo. Kawai sai harbe-harbe muka fara ji, inda muka fara gudun tsira da rayuwarmu. Sun sace mutum biyar daga wata masana’antar ruwan leda,” inji wata majiya a yankin.

Da wakilinmu ya tuntubi Kakakin ’Yan Sandan Jihar, DSP Wasiu Abiodun ya ce yana wajen taro.

Sai dai ya yi alkawarin yin magana a kai daga bisani, ko da yake har zuwa lokacin hada wannan rahoton bai yi hakan ba.