✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun sace mutane 14 a Kaduna

Mutane uku sun yi nasarar tserewa daga hannun ’yan bindigar.

’Yan bindiga sun yi awon gaba da mutum 14 a Unguwan Kabulo da ke Karamar Hukumar Chikun a Jihar Kaduna a ranar Lahadi.

Mutanen unugwar sun shaida wa wakilinmu cewar da farko mutum 17 ’yan bindigar suka dauke ciki har da mata, amma uku daga cikin mutanen sun tsere daga hannun masu garkuwar.

“Sun yi garkuwa da mutum 14 — baligai da mata da kananan yara — a gidan wani mai suna Shehu da makwabcinsa,” inji Mohammed,  wanda ya ce ya ga jirgin yaki yana shawagi a yankin.

Ya bayyana cewa an kai harin ne da misalin karfe 1:30 na daren Lahadi, wanda hakan ya tashi hankalin mutane da dama.

Ko da aka tuntubi kakakin ’yan sandan Jihar Kaduna, ASP Mohammed Jalige kan lamarin, bai amsa ba har zuwa lokacin da aka hada wannan rahoto.

Shi ma da Kwamishinan Tsaron Cikin Gida, Samuel Aruwan, bai amsa rubutaccen sakon da aka aike masa ba labarin garkuwa da mutanen.

Amma ya fitar da wata sanarwar cewar jami’an tsaro sun ceto mutane da dama ciki har da mata aka yi garkuwa da su a Unguwan Najaja da Kerawa da ke Karamar Hukumar Igabi.

Ya ce jami’an tsaro sun yi amfani da jirgin yaki wurin hallaka ’yan bindigar tare da tseratar da mutanen da aka sace din.

A cewarsa, bayan an gano maboyarsu, ’yan bindigar sun ara ana kare suka bar mutanen da suka yi garkuwa da su.

Ya kuma bayyana jinjinar Gwamna Nasir El-Rufai ga jami’an tsaron kan dakile yunkurin garkuwa da mutane da suka yi a Karamar Hukumar ta Igabi.