✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun sace matar likita da kawarta a Binuwai

An sace su yayin da matar likitan ta fito rakiyar kawar.

Wasu ’yan bindiga sun sace matar wani likita da kawarta a unguwar GRA da ke Makurdi, babban birnin Jihar Binuwai.

Wadanda suka bayar da shaida kan lamarin sun ce ya faru ne a ranar Lahadi a gaban gidan matar likitan.

  1. Atletico ta nada Fernando Torres kocin matasa
  2. An sace Sarkin Jaba da ke Kaduna

An ruwaito cewar, matar likitan da ke aiki a Cibiyar Lafiya ta Tarayya da ke Makurdi, Dokta Dzwachi, ‘yan bindigar sun yi awon gaba da su bayan ta fito rakiyar wata abokiyarta da ta kawo mata ziyara.

Dokta Dzwachi, ya tabbatar wa manema labarai a Makurdi cewa matarsa ​​na tare da kawarta lokacin da aka sace su tsakanin da misalin karfe 6:00 na yamma.

Sai dai neman jin ta bakin Kakakin ‘yan sandan Benuwai, DSP Catherine Anene ya ci tura, a yayin da ba ta amsa kiran da wakilinmu ya yi mata ba.