✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun kashe mutum 9, sun sace 20 a Kaduna

A baya-bayan nan sojoji sun kashe kasurguman 'yan bindiga a Kaduna.

’Yan bindiga sun kashe wasu mutum tara da suka hada da ’yan banga hudu a unguwar Sabon Layi da ke Karamar Hukumar Birnin Gwari a Jihar Kaduna.

’Yan bindigar sun yi ta harbe-harbe tare da kashe mutum tara kafin su yi awon gaba da wasu sama da 20 tare da wasu dabbobi.

Idan dai za a iya tunawa, dakarun Operation Forest Sanity ta sojojin Najeriya sun yi wa wani kasurgumin shugaban ’yan bindiga a jihar, Isiya Danwasa da yaransa kwanton bauna tare da kashe shi.

Bayanai sun nuna cewa Isiya Danwasa ya yi kokarin tura daya daga cikin ’ya’yansa ya sayo wasu makamai da alburusai a garin Kaduna.

Kakakin rundunar sojin, Laftanar-Kanar Musa Yahaya, ya bayyana a wata sanarwa a ranar Laraba cewa, daga bisani, sojojin sun bi sawun yaron sun kama shi, inda suka yi amfani da shi wajen kama wasu shugabannin ’yan bindiga guda biyu.

A baya-bayan nan dai jami’an tsaro na ci gaba da samun gagarumar nasara a yaki da ’yan ta’adda a Arewacin Najeriya.