✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan bindiga sun kashe mutum 17 a kauyen Kaduna

Maharan sun kai farmakin ne lokacin da ilahirin mutanen yankin suka tafi kasuwa

Wasu gungun ’yan bindiga sun kai hari a kauyen Rafin Sarki na gundumar Fatika da ke Karamar Hukumar Giwa ta jihar Kaduna, inda suka halaka mutum 17.

Shaidar gani da ido ta ta tabbatar wa Aminiya cewa harin an kai shi ne wajen misalin karfe hudu zuwa biyar na yammacin Alhamis.

Majiyar ta kara da cewa maharan sun isa kauyen ne dauke da muggan makamai inda suka yi ta harbin kan mai uwa da wabi, inda suka kashe jama’a da dama, musamman wadanda ke gonakinsu a wannan lokaci.

Majiyar har ila yau ta ce ga dukkan alamu maharan sun je daukar fansa ne saboda sun dade suna kokarin kawo farmaki a kauyen amma garin ya gagare su shiga sakamakon dagewar da matasan yankin suka yi.

A cewar majiyar, “Wannan ya sa suka yi amfani da ranar ta Alhamis domin ita ce ranar kasuwar Giwa, sa’ilin da yawancin dakarun kauye suka tafi cin kasuwa sai suka afka wa garin.

“Yanzu haka, gawarwaki 17 muka gano kuma muka yi masu suttura. Amma kuma muna ci gaba da neman sauran jama’a da yawa wanda tun da abin ya faru har yanzu ba mu gansu ba.

“Babu rahoton sace shanu ko dabbobi ko wata kone-kone, illa rashin rayuka kawai bayan harin yan taaddar,” inji majiyar.

Duk kokarin neman Kakakin Rundunar ’Yan Sanda na jihar Kaduna, Mohammed Jalige ta waya kan harin ya gagara saboda lambarsa ta ki shiga har zuwa lokacin hada wannan rahoto.