✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun kashe mutum 12 da suka fita ceton wani dan kasuwa da aka sace

Mutum 12 ne suka rasa rayukansu yayin da suka fita ceton wani dan kasuwa da ’yan bindiga suka sace a garin Amarawa da ke Karamar…

Mutum 12 ne suka rasa rayukansu yayin da suka fita ceton wani dan kasuwa da ’yan bindiga suka sace a garin Amarawa da ke Karamar Hukumar Illela ta Jihar Sakkwato.

’Yan bindiga sun harbe mutanen ne yayin da suka yi yunkurin ceto wani attajiri, Alhaji Rabi’u Amarawa da maharan suka sace a gidansa da Asubahin ranar Litinin.

Wasu ’yan uwan wanda aka sace sun ankarar da ’yan bijilanti wadanda suka hada kai suka bi sahun ’yan bindigar a kokarinsu na ceto attajirin.

Aminiya ta samu cewa ’yan bindigar babu wata-wata suka bude wuta a kan mutanen da suka fita aikin ceton, lamarin da ya sanya 12 suka mace ciki har da wani dan uwan wanda aka tafi cetowa.

“Dan kasuwar da aka sace kawuna ne kuma wasu ’yan uwana biyu na daga cikin wadanda aka kashe yayin da suka fita tunkarar ’yan bindigar.”

“Yanzu haka bamu dade da binne mutum goma ba,” a cewar wani mazaunin yankin da ya bukaci Aminiya ta sakaya sunansa.

“Kai tsaye suka je gidansa suka dauke shi tamkar shi kadai suka kawo wa takakka.”

“Sai dai a yanzu komai ya lafa a yankin wanda ke da tazarar da bata wuce kilomita daya da garin Illela ba, sai dai kowa ya zugum ana jimami.”

Kakakin rundunar ’yan sandan Jihar, ASP Sanusi Abubakar yayin tabbatar da aukuwar lamarin, ya ce an yi asara mai girman gaske sakamakon mazauna garin basu sanya jami’ansu a lamarin ba gabanin bin sahun ’yan bindigar.

Sai dai ya ce hakan ba zai sa su yi kasa a gwiwa ba a yayin da tuni bincike ya kankama kuma sun tura rukunai biyar daban-daban wanda kowannensu ya kunshe hazikan ’yan sanda 63 a yankunan da ta’addancin ’yan bindiga ya fi kamari a Jihar.

“Bamu dade ta kadamar da rundunar Puff Ader II ba kuma gwamnati ta bamu motocin sintiri 16 daga cikin 80 da gwamnan Jihar ya yi mana alkawari,” in ji ASP Abubakar.