✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun kashe manoma a Binuwe

Kisan ya jawo barkewar zanga-zanga, wadda ta yi sanadin rasa rayuwa mutum daya.

’Yan bindiga sun kashe mutum uku a yankin Yelewta da ke Karamar Hukumar Guma ta Jihar Binuwe.

Bayan mutum ukun da ake  zargin makiyaya ne suka kashe su, harsashin jami’an tsaro ya yi ajalin mutum daya daga cikin masu zanga-zanga kan kashe manoman.

Zanga-zangar ta barke ne a kan titin Makurdi zuwa Lafia, bayan samun labarin kashe manoman a gonakinsu.

Shugaban Karamar Hukumar Guma, Caleb Aba, ya shaida wa wakilinmu cewa ya ce kashe matasan da ’yan bindiga suka yi ya fusata al’ummar yankin.

Ya ce hadin gwiwar jami’an tsaro sun yi kokarin kwantar da tarzomar da ta barke a yayin zanga-zangar, amma harsashinsu ya samu mutum daya daga cikin masu zanga-zangar.

Da muka yi kokarin jin ta bakin kakakin ’yan sandan jihar, DSP Catherine Anene, dangane da lamarin, hakarmu ba ta cimma ruwa ba.