✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Yan bindiga sun kashe hakimi a Binuwai

‘Yan bindiga sun kashe Hakimin Kundav, Cif Awua Alabar da ke karamar Hukumar Ukum a Jihar Biniwai. Wata majiya a kauyen ta ce ‘yan bindgar…

‘Yan bindiga sun kashe Hakimin Kundav, Cif Awua Alabar da ke karamar Hukumar Ukum a Jihar Biniwai.

Wata majiya a kauyen ta ce ‘yan bindgar sun raunata kanin Hakimin Msoo Albar, sakamakon harbin bindiga amma an garzaya da shi asibiti.

Kawo yanzu, ba a samu cikakken bayanin yadda abun ya faru ba.

Gwamna Samuel Ortom ya yi allawadai da kisan da aka yi wa hakimin ranar Talata.

Gwamna Orton, a takardar da mai magana da yawunsa ya raba, Terver Akase, ya fitar ya nuna rashin amincewa da bakin cikin faruwar lamarin.

Ya kuma yi kira ga jami’an tsaro su gano wadanda suka aikata abun.

Ortom ya kuma yi kira ga jamma’ar gari da su taimaka wa jami’an tsaro da labarin wuraren da za su iya gano ‘yan bindigar.

Ya kuma danganta abin da ya faru da raddin ‘yan ta’adda saboda fatattakarsu da ake yi daga mafakarsu zuwa wasu sassa na kasar nan.