✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun kai hari Kudancin Kaduna

Maharan suka jikkata mutum uku.

Wasu ’yan bindiga da ba a kai ga tantance ko su waye ba sun kai hari kan Unguwar Katsit da ta Yashim a Karamar Hukumar Zangon Kataf ta Jihar Kaduna.

Wakilinmu ya ruwaito cewa lamarin ya faru ne a daren Lahadi inda maharan suka jikkata mutum uku.

Wani Dan acaba da ya sha sa kyar ya shaida wa Aminiya cewa harin ya afku ne da misalin karfe takwas na dare yayin da maharan suka fara harbi kan mai uwa da wabi.

“Ina dauke da fasinja mun zo daidai wajen gidan biredin Alpha sai muka hango mutane maza da mata kowa na ta gudun ceton rai.

“Hakan ta sa na juya da babur dina muka koma da baya zuwa barikin sojoji na Kafanchan inda muka tarar da wadansu mutanen da suka tsere can domin neman mafaka.

“A nan muka zauna har zuwa lokacin da komai ya lafa kafin muka fito daga barikin da misalin karfe tara na dare.”

Sai dai har kawo yanzu babu wani tabbaci da aka samu a hukumance da zai inganta rahoton, a yayin da hukumomi ba su ce uffan ba a kansa.

Unguwar Katsit da Unguwar Yashim da ke Karamar Hukumar Zangon Kataf suna iyaka ne da garin Kafanchan, hedkwatar Karamar Hukumar Jama’a dukkansu a yankin kudancin Jihar Kaduna.