✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Yan bindiga sun harbe mutum 8 a wajen radin suna a Burkina Faso

Wasu ‘yan bindiga sun kutsa kai harabar wani waje da gudanar da bikin radin suna a kauyen Sandiaba da ke lardin Koulpelogo na tsakiyar Gabashin…

Wasu ‘yan bindiga sun kutsa kai harabar wani waje da gudanar da bikin radin suna a kauyen Sandiaba da ke lardin Koulpelogo na tsakiyar Gabashin Burkina Faso.

Kamfanin dillancin labarai mallakin gwamnatin kasar na AIB ne ya rawaito labarin ranar Talata.

AIB ya kuma rawaito cewa  `yan bindigar da har yanzu ba a gano ko su waye ba, sun kutsa kauyen ne da ke da tazarar kilomita hudu zuwa garin Soudoughin da ke lardin na Koulpelogo ranar Litinin.

Wata majiya ta bayyana mana cewa ‘yan ta’addan sun rika harbi kan mai uwa da wabi bayan sun kutsa kai wajen wani taron, har sai da suka kashe mutum takwas.

Kazalika kamfanin dillancin labaran ya rawaito cewa duka da matakan da ‘yan sanda da sojoji suka dauka kan lamarin, har yanzu dai tsaro a lardin Koulpelogo da ma wasu yankuna da dama a Burkina Fason na halin zaman dar-dar.