✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun harbe dan Majalisar Zamfara

’Yan bindiga sun kashe Hon. Muhammad Ahmad a Jihar Katsina.

’Yan bindiga sun kashe dan Majalisar Dokokin Jihar, mai wakiltar Shinkafi, Muhammad G. Ahmad.

’Yan bindigar sun harbe dan majalisar ne ranar Talata da dare a kan hanyar Sheme zuwa Funtua a Jihar Katsina, mai makwabtaka da Zamfara.

Daraktan Yada labaran Majalisar Dokokin Jihar Zamfara, Mustafa Jafaru-Kaura, ya ce, “Yana hanyar kai dansa asibiti a Kano ne lokacin da aka kai musu harin; ’Yan bindigar sun yi garkuwa da dan nasa da direban.’’

Jihohin Katsina da Zamfara suna fama da matsalar ’yan bindiga da ke kai-komo a dajukan da suka hade iyakokinsu.

Babu cikikken bayani game da rasuwar Hon. Muhammad Ahmda, wanda Akawun Majalisar Dokokin Jihar Zamfara, Sa’idu Anka, shi ma ya tabbatar da rasuwar dan Majalisar.

Dan Majalisar mai wakiltar Zurmi, ya ce da misalin karfe 9 na dare ne aka bude mamacin wuta a kan babbar hanyar Gusau zuwa Funtua a hanyarsu ta zuwa Kano.

Sai dai ya ce dan Hon. Muhammad na hanyar raka dansa zuwa Kano ne, inda zai bi jirgi da safe domin komawa makaranta a kasar Sudan da safe.

Shi ma ya tabbatar cewa ’yan bindigar sun yi garkuwa da direban motar da kuma dan mamacin.