✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun hallaka mutum 40 a sansanin ’yan gudun hijirar kasar Kongo

Ana zargin adadin wanda suka mutu ya zarce 40.

Akalla mutum 40 ne ’yan bindiga suka hallaka a wani sansanin ’yan gudun hijira da ke Gabashin Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo bayan wani mummunan hari da suka kai.

Kungiyar da ke sanya ido a Yankin Kivu ta ce ’yan bindigar sun kai harin da wukake ne daren ranar Laraba, inda suka hallaka mutane a yankin Plaine Savo.

Jami’an yankin da kungiyoyin fararen hula sun ce adadin wadanda aka kashe ya zarta 50, yayin da kakakin sojin yankin Ituri, Laftanar Jules Ngongo, ya ce sun tabbatar da mutuwar mutum 21.

Kungiyar da ke sanya ido a kan rikicin yankin ta ce wata kungiyar ’yan bindiga da ake kira da ‘CODECO’ ce ake zargi da hannu wajen kai harin, wanda ta danganta shi da kisan kabilanci da ake fama da shi a yankin.

Yankin Djugu da ke iyaka da Tafkin Albert da kuma kasar Uganda ya zama wani dandalin zubar da jini na tsawon lokaci tsakanin ’yan kabilar Lendu da Hema.

Fada tsakanin al’ummomin ya barke ne tun a 1999 zuwa 2003, inda ya lakume rayukan dubban mutane kafin dakarun kasashen Turai su shawo kan sa ta hanyar aikin samar da zaman lafiya.

Daga bisani, tashin hankalin ya sake dawowa a 2017 wanda ake zargin CODECO da haifarwa, lamarin da ya kai ga kai hari a kan mutanen da suka rasa matsugunan sun a kwanaki 8 tsakanin watan Nuwamba da Disamban bara, ya kuma yi sanadiyar kashe mutum 123.