✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun dauke tsohon kantoma a Zamfara

Sun yi awon gaba da shi a hanyar gonarsa.

’Yan bindiga sun yi garkuwa da tsohon Kantoman Karamar Hukumar Tsafe a Jihar Zamfara, Aminu Mudi.

Aminiya ta gano cewa ’Yan bindiga sun yi garkuwa da Aminu Mudi ne a lokacin da yake kan hanyarsa ta komawa gida daga gonarsa a ranar Alhamis da yamma.

“’Yan bindiga suna kan babura, sai suka sa shi ya bi su zuwa cikin daji a kan babur dinsa sannan wasu daga cikinsu suka biyo bayansa,” inji wani ganau.

Bayanan da muka samu daga wani makusancin tsoshon shugaban karamar hukumar sun nuna cewa masu garkuwar sun sako shi.

Wani makusancin tsohon kantoman ya tabbatar mana cewa an sako shi ne da dare a ranar Juma’a.