✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga: Sheikh Gumi yana mana katsalandan – Masari

Gwamna Aminu Bello Masari na jihar Katsina, ya nuna tsagawaran adawarsa a kan tsarin da’awar da Sheikh Ahmed Gumi  ya bullo da ita wajen kawo…

Gwamna Aminu Bello Masari na jihar Katsina, ya nuna tsagawaran adawarsa a kan tsarin da’awar da Sheikh Ahmed Gumi  ya bullo da ita wajen kawo karshen ta’addancin ’yan daban daji da suka addabi yankunan Arewa maso Yammacin kasar.

Shehin malamin bayan gewayen da ya rika yi a wasu dazukan yana gana wa da ’yan daban daji domin neman samun zaman lafiya, ya roki gwamnatin Najeriya da ta yi sulhu da su ta hanyar yi musu afuwa.

Sai dai Gwamna Masara a wata hira da aka yi da shi a gidan Talabijin na Channels, ya kalubalanci Sheikh Gumi a kan da’awarsa wanda a cewarsa malamin bai gano inda bakin zaren yake ba har yanzu.

A cewar Masari babu abin da Sheikh Gumi ya sani game da fadi tashin da Gwamnonin yankin Arewa maso Yammacin kasar ke yi dangane da batun yaki da ta’addancin ’yan daban daji.

“Me ya sani game da abin da muka yi a Kaduna? Ina kalubalantar Sheikh Gumi ya fito ya fada mana abin da ya san mun aiwatar a Kaduna,” a cewar Masari.

“Labaran da yake samu a yanzu tun shekarar 2015 ake fadin su, shi suka fada a 2019. Me Sheikh Gumi ya sani game da dazuka, ko dai tausaya wa miyagu yake yi?”

A yayin da yake ci gaba da martani game da ra’ayin Sheikh Gumi kan salon da gwamnonin suka rika wajen yakar ’yan daban daji, Masari ya ce, abin da kawai malamin ya kamata ya ci gaba da yi shi ne yi wa ’yan ta’addan wa’azi da fadakar da su a kan kyakkyawar tarbiyya.

Kazalika, gwamnan ya ce baya goyon bayan katsalandan din da Sheikh Gumi yake yi a tsakanin gwamnoni da ’yan bindiga masu kashe-kashe da satar mutane gami da neman kudin fansa.