✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Yan bindiga: Gwamnatinmu ta gaza —Gwamnan Katsina

Gwamnatin Jihar Katsina ta ce ta yarda cewa ta gaza wajen magance matsalar ‘yan bindiga da ke addabar jihar. Gwamna Aminu Bello Masari ya ce…

Gwamnatin Jihar Katsina ta ce ta yarda cewa ta gaza wajen magance matsalar ‘yan bindiga da ke addabar jihar.

Gwamna Aminu Bello Masari ya ce don haka jin kunyar hada ido da jama’ar da rikicin ‘yan bindiga ya shafa saboda gwamnatinsa ba ta iya kare su.

Da yake bayani a kan hare-haren, gwamnan ya ce bai san yadda mutanen da matsalar ‘yan bindiga ta shafa a jihar Katsina za su dauki gwamantin tasa da ta kasa cika alkawain kare su ba.

Gwamnan ya ce gwamnatin jihar ta yi duk abin da ya kamata domin magance matsalar ‘yan bindigar, ciki har da bude kofar tattaunawa da yin sulhu domin wanzuwar zaman lafiya a jihar.

“Zaki ma a daji ba ya kisa sai ya ji yunwa kuma ba ya kashe daukacin dabbobi sai wanda zai iya ci a lokaci guda.

“Amma su ‘yan bindiga suna shigowa gari su yi ta harbin kan mai uwa da wabi suna kisan jama’a ba gaira ba dalili kamar yadda suka yi a baya bayan nan a sassan Faskari da Dandume inda suka yi ta kisan jama’a.

“Dan haka nace hallayarsu tafi ta dabbobi muni, Ni a ganina babu sauran wani mutumin kirki da ke zaune a daji”, inji shi.

Ya kara da cewa gwamnatinsa ta yi akalla kaso 90 cikin 100 na abun da za ta iya yi, kuma a dokar tsarin mulkin tsaro na hannun Gwamnatin Tarayya.

Akalla mutum 70 ne suka rasa rayukansu a baya-bayan nan a farmakin ‘yan bindiga a jihar Katsina.