✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga 200 sun ajiye makamai a Sakkwato

Tsoffin ’yan bindigar sun mika dabbobi 500 da suka sace tare a alkawarin sun daina

Kimanin ’yan bindiga 200 ne suka tuba tare da ajiye makamansu a Jihar Sakkwato, inda Gwamantin Jihar ke tattaunawa da su domin ganin an samu wanzajjen zaman lafiya.

Tsoffin ’yan bindigar da a baya suke kai hare-hare a yankin Gabashi jihar sun kuma mika dabbobi 500 da suka sace a baya.

Kwamishinan Tsaro na Jihar Sakkwato, Garba Moyi ta shaida wa ’yan jarida cewa wadanda suka mika wuyan sun yi alkawarin ba za su kara yin garkuwa da mutane ba.

A daya bangaren kuma an yi musu alkawarin cewa jami’an tsaro ba za su kama su ko kai musu hari ba, face sun dauke da makami ko aikata wani nau’i na manyan laifuka.

Moyi ya ce gwamnatin jihar ta ba da aikin gina madatsar ruwa a Kamarawa, saboda daukewar hare-haren ’yan bindigar da aka sasanta da su a yankin.

“Tun tuni ya kamata a fara aikin amma sabbin hare-hare da ambaliya a yankin suka hana.

“Muna kuma shirin gina gandun kiwo da makarantu domin ’yan’yansu”, inji shi.