✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yakin Sudan: ’Yan Najeriya na bi ta Saudiyya don dawowa gida

A ranar Litinin ake sa ran rukunin karshe da aka kwashe daga Khartoum za su isa Port Sudan, inda za su tsallaka zuwa Jidda

Dalibai da sauran ’yan Najeriya da suka baro Khartoum, babban birnin Sudan ranar Asabar, sun kama hanyar zuwa kasar Saudiyya domin dawowa gida.

A cikin dare ne — kafin karewar wa’adin tsagaita wuta a yakin Sudan — motocin ’yan Najeriya suka kama hanyar Port Sudan da ke iyaka da kasar Saudiyya, inda ake sa ran za su tsallaka zuwa birnin Jidda da kasar Saudiyya.

A safiyar yau Litinin ake sa ran isarsu Port Sudan zuwan Jidda, inda daga nan ake fata za su kamo hanya zuwa gida Najeriya.

Sauya hanyar maimakon bi ta kasar Masar da gwamnati ta tsara da farko na da nasaba da hana shiga kasar da hukumomi suka yi ga rukunin farko na ’yan Najeriya da suka bar Khartoum tun ranar Laraba.

Wani dalibii daga cikin ’yan Najeriya da ke kan hanarsu ta zuwa Port Sudan, ya shaida mana cewa, “Dalilin canza shi ne, har kawo yanzu kasar Masar ba su ba da damar kowa ya shiga kasarsu ba.

“Hatta wadanda suka tafi yau kwana uku suna boda amma ba su shiga ba; Kuma babu abinci, gami da sauran matsaloli.

“Shi ya sa aka ce mu tafi can (Port Sudan); Fatan da muke Allah Ya sa gwamnati ta yi abin da ya kamata, don muma har mun dauki hanya wasu suna Port sudan wasu suna Egypt za a tafi. Daga karshe shi ne aka ce mu tafi Port Sudan.”

Aminiya ta ruwaito cewa kafin yanzu, gwamnatin Saudiyya ta kwashi ’yan Najeriya da ’yan wasu kasashe sama da mutum 2,000 zuwa kasar daga Sudan bayan barkewar yakin.

Daga Jidda za a tsara yadda ’yan sauran kasashen da Saudiyya ta kwashe daga Sudan din za su koma gida.

Kiki-kaka a Masar

A halin da ake ciki, har yanzu babu tabbas game da makomar ’yan Najeriya sama da 500 da suka bar Khartoum da nufin shiga kasar Masar domin bin jirgi su dawo gida.

Najeriya ta tura jiragen soji guda uku domin kwaso ’yan kasar da suka guje wa yakin na Sudan a kasar Masar.

Hakazalika kamfanin jirage na Air Peace na zaman jira, a kowane lokaci domin ba da gudunmawar kwaso su.

Gidauniyar Dangote ma ta shiga hadin gwiwa da Gwamnatin Tarayya da kuma Air Peace domin ganin an kwaso ’yan kasar da ke Sudan a lokacin da yaki ya barke.

Sai dai kuma Ofishin jakadancin Najeriya da ke Alkahir ya ce hukumomin Masar sun ki bayar da izinin shiga kasar ga ’yan Najeriya da suka gudo daga yakin Sudan.

’Yan Najeriya sama da 500 ciki har da kananan yara da suka makale a kan iyakokin Sudan, na zaune a dokar daji, wasunsu ma kilomita 100 kafin iyakar kasar Masar.

Wasu daga cikinsu sun bayyana cewa akwai marasa lafiya a cikinsu, baya ga rashin abinci da rashin ruwa da rashin kudi da rashin layin sadarwa da suke fama da shi a dokar dajin.

Ofishin jakadancin da ke Khartoum ya ce rashin samun izinin hukumomin tsaron Masar ne ya hana ’yan Najeriyar shiga kasar, inda za su hau jirgi zuwa gida daga birnin Alkahira.

Idan ba a manta ba, Aminiya ta ruwaito yadda ’yan uwan wadanda suka makale a iyakar Sudan da Masar ke duba yiwuwar yadda matafiyan za su sauya hanya su je Port Sudan domin dawowa gida.

Wannan dori ne a kan tsaka-mai-wuya da matafiyan suka shiga a lokuta daban-daban sakamakon dambarwar kudin hayar motocin kamfanin jigilar da da aka ba wa kwangilar dauko su.

Ko a ranar Asabar, matsalar biyan kamfanin ya sa sai da motocin suka sauke matafiyan bayan an gama lodi ana jiran su tashi, kafin daga baya a sasanta.