✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yaki da ta’addanci: Najeriya za ta fara amfani da mutum-mutumi da jirage marasa matuka

Hakan wani yunkuri ne na yin amfani da fasahohin zamani don magance kalubalen tsaro.

Rundunar Sojojin Najeriya ta ce za ta fara amfani da mutum-mutumi da jirage marasa matuka wajen tattara bayanan da za su kai ga yaki da ’yan ta’adda a fadin kasar nan.

Hukumar Kula da Fasahar Sadarwa ta Kasa (NITDA), ta hannun cibiyarta da ke kula da Fasahar Zamani da Mutum-mutumi (NCAIR) ita ce ta bayyana hakan.

Hukumar ta ce hakan wani yunkuri ne na yin amfani da fasahohin zamani wajen magance kalubalen tsaron da ya addabeta.

Bugu da kari, hukumomin biyu za kuma su hada gwiwa wajen kera kayayyakin da sojoji za su rika amfani da su wajen yaki da ta’addancin.

Daraktan cibiyar ta NCAIR, Injiniya Ya’u Garba Isa ne ya bayyana hakan lokacin da ya karbi bakuncin Shugaban Makarantar Muhalli, Kimiyya da Fasaha ta Sojojin Najeriya (NACEST) da ke Makurdi, Birgediya Janar Yahaya Abdulhamid a ofishinsa da ke Abuja ranar Alhamis.

A cikin wata sanarwa da NITDA ta fitar, “Injiniya Ya’u ya ce, “Yin hadin gwiwa da sojoji zai bayar da wata muhimmiyar dama ga cibiyar ta fara sarrafa kayan aikin sojojin a gida Najeriya.”

Sanarwar ta kara da cewa cibiyar na kuma duba yiwuwar fara sarrafa gurnetin da zai rika amfani da na’ura mai kwakwalwa wajen ganowa tare kuma da tattara bayanan tsaro.

Tun da farko da yake nasa jawabin, Birgediya Janar Yahaya ya ce bukatar hadin gwiwar rundunar tasu da NITDA ta taso ne la’akari da irin gagrumin ci gaban da take kawo wa bangaren fasaha a Najeriya.