✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yajin aikin ASUU: Babu Gara Tsakanin UTAS da IPPIS —NITDA

Hukumar NITDA ta ce sau biyu ana yi wa UTAS gwajin inganci amma ba ya kai labari

Hukumar Bunkasa Fasahar Sadarwa ta Kasa (NITDA) ta ce tsarin biyan albashi na UTAS da U3PS da jami’oi ke amfani su da kuma IPPIS da Gwamnatin Tarayya ke amfani da shi, duk ba su ba su da ingnci.

Wani jami’in NITDA ya bayyana wa Majalisar Wakilai cewa IPPIS da UTAS da U3PS sun fadi gwajin da hukumar ta gudanar kan ingancinsu dangane da albashin jami’o’i.

Jami’in ya ce, bisa umarnin Gwamnatin Tarayya, sau biyu NITDA ta yi wa gwaji kan ingancin UTAS — tsarin da Kungiyar Malaman Jami’a (ASUU) ta ce dole da shi za a biya ma’aiakatan jami’a — amma babu gwajin da tsarin ya ci.

Ya bayyana cewa bayan NITDA ta yi gwajin farko UTAS ya fadi, aka bukaci ASUU ta koma ta duba, kuma ta yi, “Duk da haka, da aka yi gwaji na biyu tsari ya gaza cika sharudan da NITDA ta gindaya.”

Daga nan gwamnati ta umarci NITDA ta yi wa UTAS da IPPIS da U3PS gwaje-gwajen inganci, amma babu daya daga cikin ukun da ya cika sharuddan tsarin biyan albashin jami’o’in.

Jami’in ya bayyana hakan ne ranar Alhamis, a ci gaba da zaman Majalisar Wakilai da Shugabar Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya, Folasade Yemi-Esan da sauran jami’an gwamnati kan yajin aikin ASUU.

Shugaban majalisar, Femi Gbajabiamila ya tambayi jami’in ko NITDA ta taba bai wa gwamnati shawara ta dauki mataki kan kura-kuran da aka samu a IPPIS da take aiki da shi tun 2011 ; Jami’in ya ce NITDA ba ta da ikon yin hakan.

Gbajabiamila ya kuma tambaya ko NITDA ta kalubalanci tsarin IPPIS, wanda jami’in ya ce a’a.

Mataimakin Shugabaan Majalsar, Wase ya bayyana rashin jin dadinsa saboda NITDA ba ta dauki mataki kan IPPIS ba, inda ya ce kamata ya yi ta shawarci gwamnati kan matakin da ya dace ta dauka kan abin da ta gano.

A nata martanin, Shugabar Ma’aikatan, Folasade Yemi-Esan, ta ce Ma’aikatar Sadarwa da Tattalin Arziki na Zamani ta rubuta wa ofishinta ne bayan duba da NITDA ta yi game da IPPIS kan bukatar yin cikakken garambawul ga tsarin tsarin, kuma an kafa wani kwamiti don aiwatar da aikin. 

Ta kuma bayyana cewa IPPIS ba hanyar biyan kudi ba ne kawai, yana da bangaren gudanar da ma’aikata wanda aka umarci hukumomin gwamnati da su fara aiki da shi, kuma duk wadanda ke karkashinta sun bi umarnin.

Shugaban Hukumar Albashi ta Kasa, Ekpo Nta, ya ce hukumar ta shawarci gwamnati da ta kara albashin ma’aikatan manyan makarantu da suka hada da da jami’o’i da manyan makarantu da kwalejojin ilimi.

Ya ce gwamnati ta yanke shawarar kara albashin malaman jami’o’in da wani kaso; yayin da aka yi wa furofesoshi kari mafi yawa.

Ya musanta sanin duk wata yarjejeniya tsakanin Gwamnatin Tarayya da kungiyar ASUU na karin albashi.

Akanta-Janar na Tarayya, Sylva Okolieaboh, ya ce ma’aikaci ba shi da ikon tilasta wa wadanda ya dauke su aiki tsarin da zai biya su ba.

Don haka ya caccaki ASUU ta nacewarta a kan  dole a biya ma’aikatan jami’a da UTAS.

Majalisar ta gayyaci Ministan Kwadago da Sakataren Gwamnatin Tarayya da sauran jami’an gwamnati ne domin su bayyana a gabanta ranar Alhamis kan yajin aikin ASUU.