✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda za a nada Charles III a matsayin Sarkin Ingila

William ya zama Yariman Wales tare da matarsa Kate, matsayin Elizabeth II ta rike kafin zamanta Sarauniya shekara 70 da suka gabata

A ranar Asabar za a nada Charles III a matsayin sabon Sarkin Ingila a hukumance.

Nadin na zuwa ne bayan jawabinsa da ya yi alkawarin sadaukar da daukacin rayuwarsa wajen hidimta da al’umma, kamar yadda mahaifiyarsa ta yi.

Ya yi jawabinsa na farko tare da mika ta’aziyyarsa bayan rasuwar mahaifiyarsa, Sarauniya Elizabeth II, wadda ya yi alkawarin bin sawunta.

Charles mai shekara 73, wanda shi ne Yarima Mai Jiran Gado, ya zama Sarkin Ingila ne kai-tsaye bayan Allah Ya yi wa mahafiyarsa, Sarauniya Elizabeth II cikawa tana shekara 96.

A ranar Alhamis Sarauniya ta koma ga Mahaliccinta bayan ta shekara 70 a kan karagar mulki — Ita ce ta fi kowa dadewa a kan karagar mulki a tarihin kasar Birtaniya.

A ranar Asabar ake nada babban danta Charles III a matsayin wanda ya maye gurbinta, a wanin biki da zai gudana a Fadar St. James a birnin London.

Bikin, wanda za a yi bushe-bushe, shi ne na kan gaba a jerin abubuwan da za a shafe kwana 10 ana yi, na juyayin rasuwar sarauniya a hukumance.

Sai dai lokacin makokin da za a yi a fadin kasar Birtaniya gabanin kai sarauniyar makwancinta, zai fi haka tsawo ga iyalan gidan sarautar.

Charles III ya yi sharar fagen fara wa’adinsa ne bayan jawabinsan da aka yada ta talabijin ranar Juma’a, inda jinjina wa mahaifiyarsa bisa ‘sadaukarwarta mara misali’ a shekaru 70 na jagorancinta.

Ya ce, “Sarauniya Elizabeth II ta yi rayuwa mai nagarta bisa cika alkawari a tsawon lokaci, kuma ana matukar juyayin rasuwarta.

“Saboda haka, a yau ina jaddada muku tare da sabunta wannan alkawari nata.”

Sarkin ya kuma ayyana babban dansa William mai shekara 40, a matsayin Yariman Wales, yana mai bayyana kaunarsa ga dansa Harry da surukarsa, Meghan.

Hakan na nufin Kate, matar William ta zama Gimbiyar Wales, matsayin a baya mahaifiyar Charles da kuma tsohuwar matarsa, Gimbiya Dina suka rike a lokacin rayuwarsu.