✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda za a kula da tafin kafa a lokacin sanyi

Yadda za a kula da tafin kafa a lokacin sanyi

Kafa tana daya daga cikin abubuwan da suka kamata mu kula da su. Domin idan ba a kula da kafa ba, hakan na iya janyowa a samu kauje ko faso.

A rage dadewa a cikin ruwa idan an zo wanka.

Yana da kyau a wanke tafin kafa da ruwan dumi ba tafasashe ba. Sannan yana da kyau ana shafa mai a kafa a duk lokacin da tafin kafar ta gamu da ruwa. Sa’annan a rage sa takalma wanda iska ba za ta samu kafar ba.

  • A tsoma tafin kafa a ruwan lemun tsami na tsawon minti 10. Yin haka na fitar da matattun fata daga tafin kafa. Sannan a samu dutsen goge kafa a dirza ta.
  • Za a iya hada man tafin kafa idan aka hada man zaitun da ruwan lemun tsami ana shafawa a inda ta tsage.
  • A girgiza wannan hadin kafin a yi amfani da shi a kullum.
  • A rika shafa man basilin a tafin kafa sannan a sanya safa a kullum kafin a kwanta barci.
  • Uku bisa hudu na kofin man kwakwa da rabin na man kadanya na gyara tafin kafa. Idan aka samo su sai a hada su a narkar da su da wuta. Bayan sun narke, sai a shafa a tafin kafa sannan a sanya safa kafin a kwanta.
  • Kada a tsoma kafa a ruwa salam hakan ba tare da an yi wa ruwan wani hadi daga cikin ababen da na lissafa ba.
  • A kasance cikin shafa mai kafin a kwanta barci sannan a sanya safar kafa.