✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda za a kawo karshen rikicin Rasha da Ukraine —Xi Jinping

Ya kamata manyan kasashen duniya da ke rikici da juna su mayar da wukakensu cikin kube.

Shugaban China Xi Jinping ya bayyana cewa amfani da hanyoyi na siyasa ne kadai mafita wajen kawo karshen yakin da ake fafatawa tsakanin Rasha da Ukraine.

Hakan dai na kunshe ne cikin wata sanarwa da Ma’aikatar Harkokin Wajen China ta fitar a ranar Juma’a.

Sanarwar ta rawaito shugaban na China na cewar ya kyautu bangarorin biyu da ke kai ruwa rana da juna su hau teburin tattaunawa don kawo karshen rikicin da ke wakana tsakaninsu.

Shugaban na China dai a baya-bayan nan na kokari wajen ganin manyan kasashen duniya da ke rikici da juna sun mayar da wukakensu cikin kube.

Bayanai sun ce a kwanakin da suka gabata Xi ya shiga tsakanin Iran da Saudiyya wanda hakan ya sa suka fara shirin maido da huldar diflomasiyya tsakaninsu.

Kazalika, a ranar Juma’a ce Shugaban Faransa, Emmanuel Macron ya kammala ziyarar kwanaki uku da ya kai China, inda ya kara matsawa takwaransa Xi Jinping ya taimaka wajen kawo karshen rikicin Ukraine.