✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yadda za a kashe bashin da Buhari zai karbo

Ayyuka 15 ne za su amfana da rancen da Shugaba Muhammadu Buhari zai karbo

Fadar Shugaban Kasa ta ce ayyuka 15 ne a fadin shiyyoyi shida na Najeriya za su amfana da rancen da Shugaba Muhammadu Buhari ya nemi sahalewar Majalisar Dattawa don ya karbo.

Kakakin shugaban kasar, Mallam Garba Shehu, ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar.

Idan ba a manta ba, a farkon makon nan mai karewa Shugaba Buhari ya aike da takarda ga Majalisar Dattawa yana bukatar ta amince a karbo rancen Dala biliyan hudu, da Yuro miliyan 710, da kuma wani tallafi na Dala miliyan 125.

Takardar dai ta ce wannan rance na cikin Jadawalin Matsakaicin Zango na Karbo Bashi Daga Waje na 2018 – 2021.

Shugaban kasar ya kara da shaida wa Majalisa cewa za a karbo rancen ne daga Bankin Duniya, da Hukumar Raya Kasashe ta Faransa, da Bankin ba da Rancen Shigowa ko Fitar da Kaya na China (China Exim Bank), da Asusun Bunkasa Noma na Kasa-da-Kasa (IFAD),  da Bankin Credit Suisse na Switzerland, da kuma Bankin ba da Rance na SINOSURE da ke China.

Bayani dalla-dalla

Sanarwar ta Malam Garba Shehu ta kara da cewa wasikar Shugaba Buhari ta fayyace ayyuka 15 din da za a yi da kudin, da makasudin ayyukan, da lokacin da za a dauka ana yi, da jihohin da za su amfana, da kuma ma’aikatu da hukumomin gwamnatin da za su aiwatar da su.

Jadawalin ya nuna cewa ana sa ran Bankin Duniya zai samar da kudin ayyuka bakwai, ciki har da tallafin Dala miliyan 125 don “Samar da Ingantaccen Ilimi ga Kowa”.

Ana dai sa ran za a yi amfani da tallafin don samar da karin damar zuwa makaranta ga yaran da ke gararamba a titi da habaka rubutu da karatu a jihohin da za su amfana.

Tallafin, wanda Ma’aikatar Ilimi da Hukumar ba da Ilimi a Matakin Farko ga Kowa (UBEC) za su sarrafa shi, zai karfafa harkar ilimin firamare da karamar sakandire a jihohin Katsina, da Oyo, da Adamawa.

Bunkasa Noma

Sauran ayyukan da Bankin Duniya zai samar da kudin aiwatarwa su ne Shirin Tabbatar da Gaskiya Wajen Gudanar da Ayyuka a Jihohi, da Shirin Bunkasa Harkokin Noma da Sarrafa Amfanin Gona.

Jihohin da za su amfana da shirin na noma su ne Kogi, da Kaduna, da Kano, da Kuros Riba, da Enugu, da kuma Legas.

Ma’aikatar Aikin Gona da Raya Karkara ce za ta kula da aiwatar da shirin.

Manufar shirin dai ita ce bunkasa samar da amfanin gona a tsakanin kanana da matsakaitan manoma a jihohin da za su amfana.

Bugu da kari, Bankin Duniyar ne zai samar da kudin aikin inganta hanyoyin samar da ruwan sha da tsaftataccen muhalli a jihohin Delta, da Ekiti, da Gombe, da Kaduna, da Katsina, da Imo da kuma Filato a shekara biyar masu zuwa.

Yaki da COVID-19

A karkashin jadawalin karbo rancen, Bankin na Duniya ne zai kuma samar da kudin ayyukan da suka shafi yaki da annobar COVID-19, wadanda Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta Najeriya (NCDC) za ta aiwatar.

Ayyukan, wadanda za a gudanar a shekara biyar, za su kula da duk wata bukata da ake da ita don fuskantar kalubalen COVID-19, ciki har da samar da alluran riga-kafi.

Dadin dadawa, jihohin da ba su kasa 29 ba ne za su amfana da Shirin Karfafa Noma a Mawuyacin Yanayi wanda ake sa ran zai rage hatsaniya a kan albarkatun kasa a yankunan da ba su da danshi sosai.

Jihohin da za su amfana da wannan rancen, wanda Bankin Duniya da Bankin Zuba Jari na Turai (EIB) za su hada gwiwa su samar da shi, su ne Akwa Ibom, da Borno, da Oyo, da Sakkwato, da Kano, da Katsina, da Edo, da Filato, da Abiya, da Nasarawa, da Delta, da Neja, da Gombe, da Imo, da Enugu, da Kogi, da Anambra, da Ebonyi, da Kuros Riba, da Ondo, da Kaduna, da Kebbi, da Jigawa, da Bauci, da Ekiti, da Ogun, da Binuwai, da Yobe and kuma Kwara.