✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda ’yan sanda ke ‘garkuwa da mutane’ a Kano’

Ana zargin jami’an ’yan Sanda da hada baki suna tsare mutane musamman Fulani suna kwace musu kudade a Jihar Kano. Zargin na fitowa ne daga…

Ana zargin jami’an ’yan Sanda da hada baki suna tsare mutane musamman Fulani suna kwace musu kudade a Jihar Kano.

Zargin na fitowa ne daga wasu daga cikin mutanen da suka bayyana hakan a shirin wani gidan rediyo da ke Kanon wanda wakilinmu ya saurara.

Masu zargin su ce yawancin ’yan sandan na zuwa Kano ne daga Abuja da sunan aiki, suna bin kasuwannin Fulani suna kama mutanen da su ji ba, ba su gani ba, da taimakon ’yan sandan jihar.

Sun ce ’yan sandan kai ajiye mutanen da suka kama a caji ofis din da ke unguwar Kwakwaci inda ake bukatar ’yan uwansu su biya makudan kudaden beli.

Baya ga Babban Ofishin ’Yan Sanda na Kwakwacin da ya yi kaurin suna a wurin masu zargin, caji ofis na Dala da na Sharada ma duk suna cikin masu mugun aikin inji masu zargin.

Daya daga cikin mutanen da ya  ce ’yan sandan sun kama shi a kasuwar Kwanar Dangora, Abubakar Garba, ya shaida wa gidan rediyon cewa kwanansa 21 a caji ofis din Kwakwaci kafin a sake shi.

Ya ce ’yan sandan ba su sake shi ba sai da aka ba su N320,000 na beli, baya ga N95,000 da suka kwace na shanun da ya sayar a ranar da suka kama shi.

“Na sayar da shanu N95,000 a Kwanar Dangora, ina shirin barin kasuwa sai wani dan sanda mai suna Abdu Barumi ya tsare ni, da na tambaye shi laifina sai ya ce na zage shi, daga nan suka kama duka na.

“Wani ya ce min in yi shiru kuma yi; N95,000 din na tare da ni, sai ya kwace ya sa a cikin hularsa.

“An kai ni caji ofis din Kwakwaci sai da muka kashe N320,000 kafin su sake ni bayan na yi kwana 21”, inji Garba.

Shi ma wani wanda ya ce irin hakan ta faru da shi, Abubakar Dan Hadejia, ya ce sai da ya biya Naira miliyan daya da dubu hamsin da shida a caji ofis din Kwakwaci kafin a sake shi bayan ya shafe kwana 22 a tsare ba tare da wani dalili ba.

“Wata rana da safe ina gida aka kira ni a waya cewa in zo bakin babban titi. Da zuwa ta sai suka kama ni cewa za su kai ni Abuja, amma suka kai ni Kwakwaci na yi kwana 22.

“Sun zarge ni da mallakar bindiga sannan suka ce idan na koma gida in ba su hadin kai.

“Sun karbi N620,000 a wurina sannan da safe suka karbi N400,000 a gida bayan da suka sake ni; a ranar da suka kama ni kuma akwai N36,000 a tare da ni”, inji shi.

Wakilinmu ya tuntubi kakakin ’yan sanda na Jihar Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa domin jin ta bakin rundunar, amma jami’in ya ce zai neme shi bayan ya yi magana da Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar.

Sai dai a wani rahoto da BBC ta fitar kan zargin, rundunar ’yan sanda ta ce tana tsare da wasu jami’anta masu alaka da zargin.