✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda ’yan Kannywood ke murnar shekara 60 da samun ’yanci

Jaruman Kannywood sun bi sahun 'yan Najeriya wajen murnar zagayowar Ranar Samun Mulkin Kai

Ranar Alhamis 1 ga Oktoba Najeriya ke cika shekara 60 da samun ’yanci daga Turawan mulkin mallaka.

Mutane da dama ne daga bangarori da dama suke shagulgula tare da sanya hotunansu da tutar Najeriya domin murnar wannan rana.

Masana’antar fina-finan Hausa ta Kannywood ma ba a bar ta a baya ba, domin manyan jarumanta da kanana sun bayyana farin cikinsu a wannan rana.

Ali Nuhu, wanda ake yi wa lakabi da Sarki, ya sanya hotunansa da dama rike da tutar Najeriya, inda ya rubuta cewa, “Za a samu ’yanci na gaskiya ne kawai idan ana abin da ya dace.

“A matsayina na dan kasarmu Najeriya, ina kira da duk mu hadu mu rika yin abubuwan da suka dace domin ganin canjin da za mu samu.

Hada karfi da karfe

“Yau kasarmu ke cika shekara 60. Dole mu hada karfi da karfe domin tabbatar da nasarorinta.”

Shi kuma furodusa Naziru Danhajiya ya wallafa hotonsa ne da na Gwamnan Jihar Kano Dokta Abdullahi Umar Ganduje da Mataimakinsa Yusuf Gawuna da Tambarin Najeriya yana cewa, “Allah Ya kawo zaman lafiya da cigaba mai dorewa tare da cin moriyar kasarmu.

“Ina mika sakon taya murna ga dukkanmu na ranar samun ’yancin kai.

“Ina mai jan hankalinmu da kada mu dauki ’yancin da wasa, mu yi kokari wajen ba da gudunmuwarmu don cigaban Najeriya.”

 

View this post on Instagram

 

May there be peace and prosperity, and may we rejoice in the blessings that our country has given us. Happy Independence Day to you all! Let’s not take our independence for granted. Let’s do our part in making Nigeria a better place.

A post shared by Naziru Auwal (@nazir_danhajiya) on

Wakar Najeriya

Shi kuma Adam. A. Zango, waka ya yi mai taken Kereke jikeke domin murnar wannan rana.

Tun a farkon mako ne dai ya ce duk mai bukatar ya shiga wakar, ya sanya rigar Najeriya ko mai dauke da tambari ko alamar Najeriya.

Furodusa Abubakar Bashir Maishadda kuwa rubutawa ya yi cewa, “Kada ka yarda ka bari masu mugun zato su karya maka gwiwa su jawo maka koma-baya a lamuranka da abubuwan da ka sa a gaba.

“Ka ci gaba da dagewa wajen cimma manufofinka ta yadda wadannan masu mugun fatan za su ci kansu.

“Ina yi wa dukkan ’yan Najeriya murnar ranar samun ’yancin kai.”

Rarara fa?

Mawaki Dauda Kahutu Rarara ya sanya hotunansa dauke da tambarin Najeriya, tare da rubutun taya murnar samun ’yancin.

Yakubu Muhammed sanya wani sauti ya yi tare da hotonsa, inda ya rubuta cewa, “Ina mana murnar ranar samun ’yancin kai.”

Jaruma Nafisat Abdullahi kuma ta wallafa hoton tutar Najeriya, inda kuma ta rubuta cewa, “Ina mana murnar zagayowar ranar samun ’yanci.”

Shi ma Darakta Hassan Giggs ya rubuta cewa, “Kowane tsuntsu kukan gidansu yake yi.

“Ina alfahari da kasata Najeriya. Ina wa kasata murnar cika shekara 60 da samun ’yancin kai.”

 

View this post on Instagram

 

Proudly NIGERIA #60 ???????? #nigeriaindependence

A post shared by Official _Hassan_ giggs?? (@hassan_giggs) on

Sauran wadanda suka nuna murnarsu sun hada da jaruma Raliya Muhammad da darakta Aminu S. Bono da darakta Sheikh Isa Alolo da jaruma Amal Umar da mawaki Hamisu Breaker da sauransu.

Kada ku manta za ku iya bibiyar yadda ‘yan Najeriya ke bukukuwan cika shekara 60 da samun mulkin kai a sassa daban-daba na kasar a nan.