✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda ’yan bindiga suka sace mutum 8 a hanyar kasuwa

An yi wa musu kwanton bauna an yi awon gaba da su a lokacin da suke dawowa daga kasuwa

’Yan bindiga sun sace wasu mutum 8 a kauyen Owukpa da ke Karamar Hukumar Ogbadibo ta Jihar Binuwai.

Mazauna yankin sun ce ’yan bindiga sun yi wa mutanen kwanton bauna an yi awon gaba da su ne a yammacin ranar Lahadi lokacin da suke dawowa daga kasuwar kauyen Ahor0Ogbo, a kan hanyar Atamka-Ugbugbu, da ke Owukpa.

Tsohon Shugaban Karamar Hukumar Ogbadibo, Prince Samuel Onu, ya tabbatar da faruwar lamarin a lokacin da yake zantawa da ’yan jarida a Makurdi, babban birnin jihar.

Wakiliyarmu ta kira kakakin ’yan sandan jihar Binuwai, SP Catherine Anene, domin samun karin bayani amma jami’ar ba ta amsa wayar ba.