✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yadda ’yan bindiga suka hallaka mutum 9 a Kaduna

Hare-haren sun auku ne a kananan hukumomin Chikun, Zangon Kataf, Igabi da kuma Zariya.

Mutum tara sun bakunci lahira a hare-haren da ’yan bindiga suka kai a wasu kananan hukumomi hudu na Jihar Kaduna.

Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na Jihar, Samuel Aruwan, ya ce hare-haren sun auku ne a kananan hukumomin Chikun, Zangon Kataf, Igabi da kuma Zariya.

Aruwan ya sanar a ranar Juma’a cewa ’yan bindiga sun kashe mutum uku tare da jikkata wani a kan hanyar Birnin Gwari zuwa Kaduna da ke Karamar Hukumar Chikun, a tsakanin kauyen Buruku-Udawa.

A cewarsa, wanda ya samu raunin na samun kulawa a wani asibiti.

Mahara sun kuma kashe mutum daya a yankin Yola-Kadi da ke karamar hukumar, inda a nan ma suka jikkata mutum daya.

Sun kuma kashe mutum biyu a kauyen Sako da ke Karamar Hukumar Zangon Kataf inda aka gano gawarwaki biyu a yankin Kurfi-Magamiya.

A karamar Hukumar Zariya kuma an kashe wani magidanci a kauyen Saye.

Ya bayyana damuwar gwamnan jihar, Nasir El-Rufai, gami da addu’arsa ta samun rahama ga mamatan da kuma sauki da wadanda suka samu rauni.