✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda rasuwar Desmond Tutu ta girgiza Afirka ta Kudu

A ciki da wajen Afirka ta Kudu ana ganin Tutu a matsayin ma'aunin gaskiya

Al’ummar Afirka ta Kudu na ci gaba da jimamin rasuwar Archbishop Desmond Tutu, fitaccen malamin addinin Kirista kuma mai fafutukar kare hakkin dan-Adam, wanda ya riga mu gidan gaskiya ranar Lahadi.

Tutu, wanda mutane a ciki da wajen Afirka ta Kudu ke kwatanta shi da ma’aunin gaskiya na kasar, ya rasu a birnin Cape Town yana da shekara 90 a duniya.

“Rasuwar Archbishop Desmond Tutu wani sabon babi ne na jimami a ban-kwana da al’ummar kasarmu ke yi da fitattun ’yan Afirka ta Kudu wadanda suka gadar mana da ’yantacciyar kasa”, inji Shugaban Kasa Cyril Ramaphosa.

Ko da yake a baya-bayan nan an daina jin duriyar Tutu, ana tuna shi musamman saboda barkwancinsa da dawwamammen murmushinsa, da kuma fafutukarsa ba dare ba rana wajen yaki da rashin adalci ko wanne iri.

“Kama daga duron turjiya a Afirka ta Kudu zuwa mimbarin manyan majami’u da sauran wuraren ibada na duniya, da ma dandamalin karbar Kyautar Zaman Lafiya ta Nobel, archbishop din ya yi fice a matsayin jagoran kare hakkin bil-Adama wanda ba ruwansa da bambancin akida ko launin fata”, inji Shugaba Ramaphosa.

Alhini

Sanarwar mutuwar Desmond Tutu ta fito ne daga mukaddashiyar shugabar Asusun Archbishop Desmond Tutu, Dokta Ramphela Mamphele.

“A karshe dai ya rasu salim-alim a Cibiyar Jinya ta Oasis Frail Care dake Cape Town yana da shekara 90”, inji sanarwar.

Gidauniyar Nelson Mandela ta kwatanta Tutu da cewa, “mutum ne abin misali. Mai fikira. Jagora. Makiyayi”.

A cewar Thabo Makgoba, Archbishop na Cape Town, “lallai ne mu karrama wannan mutum mai addini…wanda alakarsa da Mahaliccinmu ce farkon rayuwarsa da karshenta.

“Ya kasance ba ya tsoron kowa; duk lokacin da ya ga an aikata ba daidai ba, ko ma wane ne ya aikata, zai fada.

“Ya kalubalanci duk tsare-tsaren da ke kaskantar da mutuncin dan-Adam”.

’Yan wasan kurket na Afirka ta Kudu sun daura bakin kyalle a damatsansu yayin wasansu da tawagar ’yan wasan Indiya don jimamin mutuwar Desmond Tutu.

Kwanciyar asibiti

A karshen shekarun 1990 ne aka bayyana cewa Archbishop Tutu yana da cutar kansa; a shekarun baya-bayan nan kuma, kamar yadda jaridar The Guardian ta Birtaniya ta rawaito, an sha kwantar da shi a asibiti saboda wasu larurori masu alaka da maganin da ake yi mishi.

Kamfanin dillancin labarai na Faransa, AFP, ya rawaito cewa marigayin ya bayyana a bainar jama’a bara, lokacin da aka tura shi a kan keken daukar marasa lafiya ya je aka yi mishi allurar riga-kafin COVID-19.

Sai dai a lokacin bai ce uffan ba.

An haifi marigayin ne a wani karamin gari da ke yamma da birnin Johannesburg mai suna Klerksdorp, ranar 7 ga watan Oktoban 1931.

Ya samu horo na malanta, amma bacin rai game da rashin ingancin tsarin ilmantar da ’ya’yan bakar fata ya sa ya sauya alkibla ya zama malamin addini.

Ya zauna a Birtaniya na dan lokaci, inda ya ce yakan nemi a yi masa kwatancen hanya duk da ba ya bukatar haka don kawai ya ji dan sanda farar fata ya ce mishi “Sir” – wato Yallabai.

Fafutuka

Desmond Tutu da Nelson Mandela
Desmond Tutu da Nelson Mandela a 2008 (Hoto: Themba Hadebe/AP daga The Guardian UK)

Tutu ya kalubalanci manufofi da dama a kan batutuwan da suka shafi bambancin launin fata, da luwadi, da akida.

A 1986 ya zama archbishop, ya kuma yi amfani da mukaminsa wajen kiraye-kirayen kakaba takunkumi a kan tsarin mulkin wariyar launin fata, daga bisani kuma ya shiga fafutukar kare hakkokin mutane a fadin duniya.

A cewar jaridar The Guardian ta Birtaniya, Tutu ya kasance yana nesanta kansa da ANC, jam’iyyar da ta jagoranci fafutukar kwatar ’yanci ta kuma kwashe shekara fiye da 20 tana mulkin Afirka ta Kudu.

Ya kuma ki ya goyi bayan gwagwarmaya da makamai, kamar yadda ya ki goyon bayan shugabannin ANC ba tare da sharadi ba, ciki har da Nelson Mandela.

Sai dai kuma, kamar Mandela, burin Tutu shi ne samar da kasa wadda dukkan al’ummomi za su rayu tare a cikinta ba tare da tsangwama ko kyamar juna ba.

An kuma ce shi ya kirkiri kalmar “Rainbow Nation” (Alumma Bakan-Gizo) don siffanta wannan kasa.

Binciken Gaskiya

Bayan Afirka ta Kudu ta samu ’yanci daga mulkin wariya, Nelson Mandela ya nada Desmond Tutu shugabancin Hukumar Binciken Gaskiya da Sasantawa, don bin diddigin zarge-zargen take hakkin bil-Adama a zamanin mulkin wariya.

Abubuwan da ya rika ji a lokacin sun sa Desmond Tutu yana dafe kai ya fashe da kuka yayin da miliyoyin mutane ke kallo a akwatunan talabijin.

Saboda yadda ya rika sukar ANC, da farko an ki a gayyaci Tutu jana’izar Nelson Mandela a 2013, lamarin da ya jawo Allah wadai daga jama’a.

Mandela da Tutu abokai ne, kuma gidajensu ba su da nisa a Soweto.

Mandela ya taba cewa, “Har abada muryar Desmond Tutu muryar marasa galihu ce”.

Tuni dai Desmond Tutu ya ce ya shirya mutuwa, kamar yadda ya bayyana a wata makala da ya rubuta a jaridar The Washington Post a 2016: “Na shirya wa mutuwata, kuma na fayyace karara cewa ba na so a yi amfani da na’urori don taimaka min na ci gaba da rayuwa”.