✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda na sha da kyar a rikicin Hausawa da Gbagyi a Abuja —Dan gwangwan

Rigimar ta faro ne tun ranar Asabar, amma sai ranar Litinin sojoji suka samu nasarar shawo kanta

Wani mai sana’ar gwangwan ya shaida wa Aminiya yadda ya tsallake rijiya da baya a rikicin da ya barke tsakanin ’yan kabilar Gbagyi da Hausawa a Abuja.

Abba, wanda mafarauci ne da ke sana’ar gadi, ya shaida wa Aminiya cewa da kyar ya tsira da ransa bayan wasu mutane kimanin ashirin sun yi kai masa farmaki.

Ya bayyana cewa duk da cewa ya tsallake rijiya da baya, amma wadanda suka kai masa harin sun kashe masa karnuka goma sha biyar a yayin tsahin-tsahinar.

Ya ce rigimar ta faro ne tun ranar Asabar, amma sai zuwa ranar Litinin sojoji suka samu nasarar shawo kanta.

Rikicin ya samo asali ne daga wani samame da jami’an tsaro suka kai a matattarar masu shaye-shayen miyagun kwayoyi a yankin kauyen Gwarimpa da ke Abuja, amma ya rikide zuwa na kabilanci.

An tabbatar da mutuwar mutum guda dan asalin Jihar Kano mai suna Isiaka Ibrahim, sai kuma wasu da aka raunata.

An kuma lalata dukiyoyi, da suka haɗa da baburan A Daidaita Sahu guda goma Sha xaya, da kuma wasu bacoci na sana’a.

An kuma farfasa gilasan motoci kimanin goma sha takwas da aka ajiye a gaban shaguna.

Motocin wanda mallakin masu haya a shagunan ne, an lalata su ne kan zargin hada baki a tsakanin masu su da kuma wadanda su ka basu hayan shagunan, wato ’yan asalin yankin na Abuja.

Tuni dai rigimar ta lafa bayan jami’an tsaro sun shawo kanta, sai dai har izuwa ranar Talata lokacin da wakilinmu ya zaiyarci yankin ba a kai ga bude yawancin shaguna a yankin ba.

Ga bayanin bidi’o da wani daga cikin wadanda suka tsira daga harin ya shaida wa Aminiya irin asarar da ya yi, na karnuka shabiyar, da kuma yadda ya tsira daga harin mutum sama da ashirin.