✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda mutanen gari suka kare kansu daga harin ‘yan bindiga a Zamfara

Mazauna kauyen Kagurki dake karamar hukumar Kaura Namoda a jihar Zamfara sun kare kansu yayin da 'yan bindiga suka kai musu farmaki

Mazauna kauyen Kagurki dake karamar hukumar Kaura Namoda a jihar Zamfara sun kare kansu yayin da ‘yan bindiga suka kai musu farmaki.

Lamarin ya faru ne yayin da daya daga cikin ‘yan bindigar ya shiga shagon wani mutum mai sayar da kayayyaki, inda a nan take mai shagon ya umarce shi ya fice bayan ya fahimci abinda suke shirin kullawa a garin.

Wani mazaunin kauyen da bai so a bayyana sunansa ba ya tabbatarwa da Aminiya cewa hakan ce ta sa mutanen garin suka yi ta masa wajen fara ba-ta-kashi da maharan.

A cewarsa, “Daya daga cikin ‘yan bindigar ya shiga shagon wani mutum yana waya, sai mutumin yace ya fita daga shagon ko yayi maganinsa”.

“Dan bindigar yaki fita daga shagon, shi kuwa mai shagon ya dauki sanda ya fara dukansa, hakan ya fusata ragowar ‘yan uwansa, sai suka tafi suka dawo dauke da bindigogi suka fara harbi kan mai uwa da wabi.”

“Nan take muka far musu, aka dinga dauki ba dadi. Sun kashe mana mutane biyu, mu ma mun kashe musu mutum daya,” inji shi.

Sai dai daga bisani an girke jami’an tsaro domin baiwa mutanen kauyen tsaro.

Ya lokacin hada wannan rahoto, wakilinmu ya gaza samun kakakin hukumar ‘yan sandan jihar, SP Muhammad Shehu a waya, domin jin ta bakinsa dangane da lamarin.