✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda muka dakile yunkurin sace dalibai a makarantar ’yan Turkiyya a Kaduna – Sojoji

“Gamayyar dakarunmu yanzu haka suna nan sun yi wa dazukan da maharan suka gudu da daliban kofar rago.”

Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya shiyya ta daya dake Kaduna ta ce ta dakile wani yunkurin sace dalibai daga makarantar Sakandiren ’Yan Kasar Turkiyya dake Rigachikun a jihar ta Kaduna.

A wata sanarwa da Daraktan Watsa Labarai na rundunar, Mohammed Yerima ya fitar ranar Juma’a, ya ce dakarunsu sun yi wa makarantar garkuwa bayan samin wasu bayanan sirri.

Yerima ya ce dakarun nasu na tsaka da gadin makarantar ne lokacin da wasu ’yan bindiga suka wuce suka kutsa kai zuwa Makarantar Kula da Gandun Daji ta Tarayya dake Afaka a yankin Karamar Hukumar Igabi ta jihar.

Ya ce, “Bayan mun sami bayanan sirri kan yunkurin bayarin na sace daliban, nan da nan dakarunmu suka bazama don yi wa makarantar garkuwa daga maharan.

“Sai dai muna cikin tsaron makarantar ne kuma sai ga wani kiran gaggawa cewa ’yan bindigar sun mamaye waccan makarantar ta Gandun Daji da nufin sace dalibai da malamai. Daga nan ne dakarun namu suka dunguma zuwa wajen inda kuma suka yi ba-ta-kashi da su.

“An ce ’yan bindigar sun sami damar shiga makarantar ne bayan sun balle katangarta.

“Daliban da muka sami cetowa yanzu haka suna can a wani kebabben wuri, wadanda kuma aka jikkata yanzu haka na can a wani asibitin sojoji suna samin kulawa,” inji Yerima.

Ya ce gamayyar dakarun rundunonin sojojin kasa da na sama da ’yan sanda da kuma na DSS yanzu haka suna nan sun yi wa dazukan da maharan suka gudu da daliban kofar rago da nufin ganin sun ceto su.