✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda masu zanen batanci ga Annabi su biyu suka mutu a cikin wata uku

Yadda masu zanen batanci ga Annabi su biyu suka mutu a cikin wata uku.

Dan kasar Sweden din nan da ya yi zanen batanci ga Annabi Muhammadu (SAW), Lars Vilks ya riga mu gidan gaskiya.

Kafar labarai ta Aljazeera ta ruwaito kafafen labaran kasar suna bayyanawa cewa, Lars Vilks da ya yi zanen batancin ta hanyar zana abin da ya kira kan Manzon Allah a kan gangar jikin kare ya babbake a wani hadarin mota.

Rahotanni sun ce Lars Vilks yana tafiya ce a cikin wata motar ’yan sanda marar fenti inda ta yi taho-mu-gama da wata babbar mota a kusa da garin Markaryd da ke Kudancin Sweden.

’Yan sanda biyu da suke kula da shi ma sun rasu a hadarin sannan direban babbar motar kuma ya jikkata.

Bayanai sun ce motarsu ta bar birnin Stockholm zuwa Kudu inda ta kauce daga hannunta ta fada hanyar da babbar motar take , inda suka yi taho-mu-gama suka kama da wuta.

’Yan sanda sun ce ba su san dalilin da ya sa motar ta bar hannunta zuwa gefen da ba nata ba, amma suna bincike ko tayar motar ce ta fashe.

Lars Vilks, mutumin da ya yi zanen batancin
Lars Vilks, mutumin da ya yi zanen batancin

Lars Vilks mai shekara 75 yana karkashin kulawar ’yan sanda ne saboda barazanar da ya yi ta samu bayan yin zanen batancin.

Zanen wanda aka wallafa a shekarar 2007, ya harzuka Musulmi a sassan duniya, kuma ya yi zanen ne shekara daya bayan da wata jaridar kasar Denmark ta wallafa zanezanen Manzon Allah da Musulmi suka dauka babban laifi ne.

’Yan sandan ba su bayyana sunayen wadanda suka mutu a hadarin ranar Lahadin ba, amma budurwar Vilks ta tabbatar da mutuwarsa ga jaridar Dagens Nyheter.

Wata sanarwa daga ’yan sanda ta ce har yanzu ba a san yadda hadarin ya faru ba, amma alamu sun nuna ba wani ne ya kitsa shi ba.

Zanen batancin ya jawo tashin hankalin da sai da Firayi Ministan Kasar na wancanlokaci, Fredrik Reinfeldt ya gana da jakadu 22 na kasashen Musulmi, a wani kokari na yayyafa wa lamarin ruwan sanyi.

Jim kadan bayan haka ne, Kungiyar Alka’ida a kasar Iraki ta sanya tukuicin Dala dubu 100 (kimanin Naira miliyan 41 zuwa miliyan 50) ga duk wanda ya kashe shi.

A shekarar 2015, Vilks ya halarci wata muhawara a kan ’yancin fadin albarkacin baki don tunawa da fatawar a kashe Salman Rushdie, inda aka kai harin bindiga a wurin a birnin Copenhagen.

Kuma ya ce mai yiwuwa shi aka so kashewa a harin, wanda ya yi sanadin mutuwar wani daraktan fim.

A ranar Lahadi 17 ga Yunin bana ma sanannen mai zanen shaguben nan a jarida, dan kasar Denmark, Kurt Westergaard, wanda ya yi zane-zanen Annabi Muhammad (SAW) da suka janyo ce-ce-ku-ce, ya mutu yana da shekara 84 bayan ya yi fama da jinya, kamar yadda iyalansa suka shaida wa jaridar Berlingske.

Kurt Westergaard ya fara zanen barkwanci ne a jaridar Jyllands-Posten a farkon 1980, amma zanen batancin da ya yi ga Annabi (SAW) a shekarar 2015 ne ya sa aka ji sunansa a wajen kasarsa, inda bayan wallafa zanen a jaridar a shekarar 2016 Musulmi suka yi ta zanga-zangar da ta rikide tashin hankali a kasashe da dama.

Shi ne ya yi zane-zanen barkwanci 12 masu cike da ce-ce-ku-ce da jaridar ta wallafa, wadanda suke sukar Musulunci, lamarin da ya jawo kai hare-hare a ofisoshin jakadancin Denmark, kuma mutane da dama suka mutu a zanga-zangar da suka biyo baya.

Kurt Westergaard
Kurt Westergaard

Sake wallafa zanen a mujallar zambo ta kasar Faransa wato Charlie Hebdo a shekarar 2015 ya sa an kai wa ofishinta hari inda masu kishin Musulunci suka kashe mutum 12.

A baya an yi hakon Westergaard domin kashe shi, kuma ala tilas ya karasa rayuwarsa a wani mazauni na sirri tare da kariyar ’yan sanda.

Da yake magana da Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters a 2008, Westergaard ya ce ba ya da-na- sanin zanen batancin da ya yi.

Ya ce zanen ya jawo “muhawara mai muhimmanci” kan matsayin Musulunci a kasashen Yamma.

“Zan sake yin abin da na yi saboda ina ganin wannan rikicin zanen barkwancin hanya ce ta karfafa yadda za a rage rungumar akidun Musulunci,” inji shi.

Sai dai kuma ya sheka Lahira ba tare da Allah Ya ba shi damar sake wani zanen ba.