✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda ‘Mai dalilin aure’ ke share hawayen manema aure a Kano

“Duba da yadda na fuskanci mutuwar auren har guda biyu da na yi a baya don haka na kasa samun karfin gwiwar fuskantar wata mace…

“Duba da yadda na fuskanci mutuwar auren har guda biyu da na yi a baya don haka na kasa samun karfin gwiwar fuskantar wata mace da sunan aure har sai lokacin da na hadu da Malam Rabiu Ado wanda ya hada ni da matar da nake tare da ita a yanzu  ta hanyar aikinsa na daliln aure kimanin shekaru uku da suka wuce”.

Wannan bayani ne daga Malam Yarima Muhammad wanda ya yi aure ta hanyar ‘dalilin aure’.

Malam Muhammad wanda a yanzu yake da yaya biyu ya shaida wa Aminiya cewa ya samu haduwa da matarsa lokacin da ya ga wani allon talla da ke dauke da sunan Malam Rabiu Ado wanda ke nuni da adireshinsa da kuma aikin da yake yi na dalilin aure.

Ya ce ya kira lambar wayar Malam Rabiu lamarin da ya kawo karshen rayuwar da ya shiga a baya tare da matan da ya aura guda biyu inda a yanzu ya zama cikakken mai aure da ke zaune lafiya da iyalinsa.

Muhamamd daya ne daga cikin daruruwan mutanne da suka yi aure ta wannan hanya ta dalilin aure, inda suka auri matayensu ta dalilin Malam Rabiu Ado Indabawa da ya shekara biyar yana gudanarwa.

Malam Rabi’u Ado Indabawa da aka fi sani da mai dalilin aure

A cewarsa a kullum akan sami akalla mutum 50 zuwa 70 da suka hada da maza da mata da ke zuwa wurin Malam Rabi’u Ado don neman abokan rayuwa.

Ba wai mutane da kansu ne kawai ke kansu ba, su ma iyaye a nasu bangaren sukan kai yayansu wadanda suka isa aure ga Malam Rabiu don nema musu abokan rayuwa.

Malam Rabiu Ado wanda zai kai shekaru 50 da haihuwa ya bayyana cewa ya shiga wannan sana’a ce duba da yawan mutuwar aure da ke faruwa a Jihar.

Binciken Aminiya ya gano cewa a duk mako akan daura akalla aure biyar wanda ma’arautan suka hadu ta wananna hanya ta dalilin aure.

Ada ana gudanar da wanan abu na dalilin aure a sirrance, inda mutane kadan ne ke da masaniya a kanta, ta yadda manyan mata ke gudanar da ita ta hanyar yawo gidajen makwabta suna karbar hotunan mata suna tafiya da su wajen taruwar jama’a don nema musu abokan rayuwa.

Wanann abu ya dade ana yin sa a cikin garin Kano har zuwa lokacin da Malam Indabawa fara amfani da na’urorin zamani wajen gudanar da wannan lamari.

Malam Rabiu Indabawa yana amfai da allunan talla da ya kakkafa a wurare daban-daban da ke fadin jihar.

Allunan da ke dauke da sunansa da lamabar wayarsa na sanar da jama’a cewa mai neman aure budurwa ko bazawara ya kira layin waya da ke kasa don karin bayani.

“Idan mai bukata ya kira ni a waya kasancewar ina da wata sana’ar sai mu sanya lokacin da za mu hadu mu tattauna a kan abin da yake bukata na game da shekaru da matakin ilimi da taribiyya.

“A wannan hira da muke yi nake gane yanayin mutum. Idan na gamsu da shi to zan ba shi lambar wayar irin matar da ya bayyana min yana da muradi, inda zai kira ta su yi magana.

“To kai kuma daga wannan hirar da za ku yi za ka gane ko ta dace da ko akasin haka. Daga nan sai su sa lokacin haduwa har idan Allah Ya tabbaatr ya je ya samu iyayenta a yi maganar aure”, inji shi.

Malam Rabiu ya kara da cewa “daga wanann lokaci kuma aikina ya kare domin gaskiya ba na bin mutum idan zai je wajen iyayen matar da zai aura.

“Sai dai idan iyayen ne suka kawo min nema wa yayansu mazajen aure, wanda mun yi shi sosai muna kuma kan yi.

“Mutane da dama sun yi aure har da ’ya’ya ta wannan hanyar. Ba zan iya kididdige yawan mutanen ba amma a shekaru biyar din nan duk mako sai an yi aure uku zuwa biyar ta wanann hanya”.

Da aka tambaye shi ko yana karbar wasu kudi a kan wannan aiki sai Malam Rabiu ya bayyana cewa “ba na neman a ba ni ko kwabo idan ka ga abin da na yi ya cancanci ka yi min kyauta to za ka iya zuwa daga baya ka ba ni abin da ka yi niyya.

“Na sami kyaututtuka da dama ta dalilin wannan aiki amma dai ba na neman wani abu a wurin kowa; Ban shiga wanann abu don na tara dukiya ba, na yi ne don taiamakon al’umma. Ina son duk wanda yake neman abokin rayuwa ya samu”.

  • Abin da ke kawo mace macen aure

Malam Rabiu ya bayyana rashin fahimtar abin da aure ke nufi shi ya janyo mace-macen aure yake kara yawaita a fadin jihar.

Ya yi kira ga iyaye da su sami lokacin da za su rika koyar da ’ya’yansu game da rayuwar aure.

“Burina shi ne nan gaba na bude makarantar bayar da horo kan aure don koyar da mata da maza game da yadda rayuwar aure take.

“Ko a yanzu ina mayar da hankali kan mata. Sai dai wannan ba zai wadatar ba domin kamata ya yi a hada ma’auratan biyu a koyar da su kafin a daura auren”.

  • Kalubale daga dama da hagu

Malam Indabawa ya bayyana cewa yana fuskantar kalubale daga masu badala a jihar inda suke kiran sa a waya don ya sama musu matan da za su yi lalata da su.

“A wasu lokutan a rana sai  a kira ni sau 50 zuwa 70, amma za ka iske wasu kiran na maza ’yan sharholiya ne wadanda ke son matan banza. Akwai wani da ya  kira ni a waya ya nemi na tura masa mata otel.”

Indabawa ya bayayan cewa yana fuskantar kalubale inda wasu matan suke makalewa sai shi za su aura.

“Zan iya tunawa na sami mata uku da suka nuna sha’awarsu a kaina. Kai daya daga cikinsu sai da ta bayyana cewa ai ita ta ga mijin aure domin ni na yi mata”.

  • Dalilin aure ba laifi ba ne —Ustaz Ali

Yayin da yake magana da Aminiya, wani malamin addinin Musulunci a Jihar Kano, Ustaz Ali Dan Abba ya bayyana cewa babu laifi a wanann aiki a Musulunci matukar suwadanda za su yi auren sun tsaya a kan dokokin Musulunci.

“Abin da shi mai dalilin auren zai tabbatar shi ne ya tabbatar ba a zo da yaudara a cikin harkar ba.

“Ya kuma tabbatar daya daga cikin masu neman auren bai yi amfani da shi wajen cimma wata boyayyiyar manufarsa ba”, inji shi.

Ustaz Dan Abba ya bayyana cewa wannan abu ya dade ana gudanar da shi a cikin addinin Musulunci da kuma harkar gargajiya.