✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda lissafin siyasar Kano ya canja a mako guda

Shekarau da Kwankwaso sun hade a NNPP, Ganduje ya bar wa Barau Jibril takarar Sanata

Akwai wata magana da ake yi cewa “siyasar Kano sai dan Kano”, lura da irin yanayin siyasar wanda ya saba da na sauran jihohi da kuma irin rigingimunta.

Ga duk mai bibiyar abubuwan da suke faruwa yau da kullum zai tabbatar da hakan musamamn idan ya dubi yadda a ’yan kwanakin nan siyasar Kano ke samun sauyi tare da daukar sabon salo.

Wannan kuwa ya samo asali ne daga canja shekar da wadansu ’yan siyasar jihar suka rika yi daga jam’iyyun da suke ciki zuwa wasu.

Za a iya cewa yawancin masu canja shekar suna yi ne ko dai sakamakon an bata musu a jamiyyun nasu na baya, ko kuma wadancan jam’iyyun sun hana su wata dama da suke bukata.

Rikicin cikin gida a APC

Galibi dai ’yan siyasar da ke canja shekar za ka tarar sun fito ne daga jam’iyya da ke mulkin jihar, wato Jam’iyyar APC, inda suka koma sabuwar jam’iyyar nan da Madugun Kwankwasiyya, tsohon Gwamnan Jihar Kano, Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso ya farfado da ita, wato NNPP mai alamar kayan marmari.

Idan muka dauki wadansu kusoshi a Jam’iyyar APC wadanda suka samu rashin fahimta da Gwamnan Jihar Dokta Abdullahi Umar Ganduje a kan wanda ya dace ya shugabanci jam’iyyar, yayin da a tsaginsu ke ganin cewa babu wanda ya dace ya jagoranci jam’iyyar sai Alhaji Haruna Danzago, a bangaren Gwamnan Ganduje kuma sun dage ne sai Alhaji Abdullahi Abbas.

Hakan ya janyo suka kafa wata kungiya mai sunan G7 a karkashin jagorancin Sanata Ibrahim Shekarau da suka hada da mambobin kamar su Sanata Barau Jibrin da ’yan Majalisar Wakilai, Abdulkadir Jobe da Alhaji Nasiru Gabasawa da Haruna Dederi (APC-Karaye/ Rogo) da Sha’aban Sharada da Shehu Dalhatu da sauransu.

Hakan ya sa kowane bangare ya gudanar da zabensa daban.

Bayan wannan zabe ne sai uwar Jam’iyyar APC ta Kasa ta tabbatar wa Abdullahi Abbas shugabancin jam’iyyar lamarin da ya sa bangaren G7 suka nuna rashin amincewa tare da kai tsagin Ganduje a kotu aka yi ta tafka shari’a har zuwa Kotun Koli inda tsagin Gwamna Ganduje ya yi nasara.

Kafin kaiwa ga wannan matsayi shugabannin Jam’iyyar APC a matakin kasa sun yi ta kaiwa suna komowa don ganin an sulhunta bangarorin biyu sai dai hakan bai yiwu ba sakamakon sharuddan da tsagin G7 suka gindaya ciki har da batun sai an ba su kashi 55 na shugabancin jam’iyyar sharuddan da tsagin Gwamna Ganduje ya ki amincewa da su.

Tun daga wancan lokaci mambobin G7 suka fara neman madafa, saboda sun san ba za su sake zama da Gwamna Ganduje a cikin Jam’iyyar APC lami lafiya ba.

Ko kuma idan sun zauna Gwamnan ba zai ba su damar tsira da kujerun da suke kai a zaben badi ba.

Guguwar sauya sheka a Kano

A ranar 6 ga Mayu ne wadansu mambobin Majalisar Dokokin Jihar Kano suka fice daga Jam’iyyarsu ta PDP, wadanda suka hada da Isyaku Ali Danja (Gezawa) da Umar Musa Gama (Nasarawa) da Aminu Sa’adu Ungogo (Ungogo) da Lawan Hussain Chediyar ’Yan Gurasa (Dala) da Tukur Muhammad (Fagge) da Mu’azzam El-Yakub (Dawakin Kudu) da Garba Shehu Fammar (Kibiya) da Abubakar Uba Galadima (Bebeji) da Mudassir Ibrahim Zawaciki (Kumbotso) da Ali Isa (Bagwai/ Shanono)

Washegari kuma sai wadansu ’yan majalisar uku suka canja sheka daga jam’iyya mai muki ta APC zuwa Jam’iyyar NNPP, wadanda suka hada da Abdullahi Iliyasu Yaryasa (Tudun Wada) da Muhammad Bello Butu-Butu (Tofa/Rimin Gado) da Kabiru Yusuf Isma’il (Madobi).

Daga baya sai Mataimakin Shugaban Majalisar Dokokin wanda dan Jam’iyyar APC ne Zubairu Hamza Masu (Sumaila).

Baya ga wadanan an samu wata tirjiyar daga wasu jiga-jigan Jam’iyyar ta APC da suka fito daga Kano ta Kudu inda suka fice daga jam’iyyar zuwa NNPP sakamakon zargin Gwamna Ganduje da kin ba yankinsu takarar Gwamna inda suka ce yankin nasu bai taba samun kujerar Gwamna ba a wannan Jamhuriyya ta Hudu.

Wannan kuwa ya faru ne jim kadan da nuna Mataimakinsa Dokta Nasiru Yusuf Gawuna tare da tsohon Kwamishinan Kananan Hukumomin Jihar Murtala Sule Garo a matsayin wadanda za su gaji kujerarsa.

Wadannan mutane sun hada da Alhaji Alhassan Rurum (Wakilin Rano da Kibiya a Majalisar Wakilai) wanda ya nuna sha’awarsa ta takarar Gwamna.

Haka shi ma tsohon Mashawarcin Shugaban Kasa, Alhaji Kawu Sumaila ya so yin takarar Sanatan yankinsa sai dai ya fahimci cewa hakarsa ba za ta cim ma ruwa ba saboda Gwamna Ganduje ya fi karkata ga Sanatan da ke kai wato Sanata Kabiru Gaya.

A daya bangaren kuma, Gwamna Ganduje da Shugaban Jam’iyyar ba su goya wa Abdulmuminu Jibrin Kofa baya ba a neman komawa kan tsohuwar kujerarsa da yake yi ta mazabar Kiru da Bebeji a Majalisar Wakilai inda suka nuna sha’awar goya wa abokin karonsa, Kwamishinan Ilimi Dokta Sanusi Kiru baya.

Ana cikin hakan sai ga wani da ake ganin na jikin Gwamna Ganduje ne wato Shugaban Ma’aikatan Gidan Gwamnati, Alhaji Ali Haruna Makoda ya ajiye mukaminsa ya koma Jam’iyyar NNPP tare da mutanensa da suka hada da dan majalisa Badamasi Ayuba (Dambatta/Makoda) da Ahmed Speaker (Tsohon Oditan Jam’iyyar APC) da Najib Abdussalam (Shugaban Matasa na shiyya a APC) da Umar Maitsidau (tsohon Shugaban Karamar Hukumar Makoda) da Halliru Maigari (tsohon wakilin Rimin Gado/ Tofa a Majalisar Dokoki) da Hafizu Maidaji (tsohon wakilin Dambatta a Majalisar Dokoki) da Safiyanu Harbau (tsohon wakilin Tsanyawa/Kunchi a Majalisar Tarayya) da Habiba ’Yandalla (tsohuwar Shugabar Mata ta APC a Kano).

Ana ganin cewa wannan kware baya da na hannun daman Gandujen ya yi wato Ali Makoda ta samo asali ne daga hana shi ajiye aiki da Gwamnan ya yi lokacin da ya nuna sha’awarsa ta tsayawa takarar wakilin Makoda da Dambatta a Majlisar Wakilai, inda Gwamnan ya nuna yana da wanda zai tsayar a takarar tare da shawartar Alin ya ci gaba da zama a matsayinsa na babban yaronsa.

A yanzu haka wadansu daga cikin mambobin Kungiyar G7 ta su Malam Ibrahim Shekarau ta fara fita daga Jam’iyyar APC tare da samun gurbi a Jam’iyyar NNPP.

Wannan ya hada da Tijjani Jobe dan Majalisar Wakilai na Tofa/Dawakin Tofa, tun shekarar 2007.

Za a iya cewa tun bayan zaben 2019 aka fara samun rashin fahimta a tsakanin Jobe da Gwamna Ganduje inda a shekarar 2020 sai da ta kai Gwamnan ya ba shi umarnin ya dakatar da wani aikin mazabu da yake gudanarwa a hanyar Rimin Gado.

An dai ce yayin da Joben ke neman zarcewa a kujerarsa karo na biyar a gefe guda kuma Gwamna Ganduje yana so ya ba dansa Abba Ganduje takarar kujerar da ce.

A yanzu haka dai Jam’iyyar APC na cikin kaduwar rashin jiga-jigai daga cikin ’ya’yanta, wanda ya sa ta dauki matakin sulhu da sauran mambobinta da suke ganin an bata musu a jam’iyyar domin kai jam’iyyar ga gaci.

Ganduje da Barau sun daidaita

A ranar Litinin 16 ga Mayu, Gwamna Ganduje wanda ya nuna sha’awar tsayawa takarar Sanata a Kano ta Arewa ya janye ya bar wa Sanata Barau Jibrin da ke kan kujerar.

Tunda farko Sanata Barau ya nuna sha’awar tsayawa takarar Gwamna lamarin da ya janyo aka yi ta kai ruwa rana a tsakaninsa da Gwamna Ganduje har ya nade kayansa daga gaban Gwamnan, kafin a sulhunta a tsakanin Gwamnan da Sanatan wadanda suka fito daga yanki guda.

Haka Gwamna Ganduje ya rika zuwa gidan Sanata Shekarau don sulhuntawa a daidai lokacin da aka yi ta yada jita-jitar Sanatan yana tattara kayansa don ficewa daga Jam’iyyar APC zuwa NNPP.

Haka rahotanni sun ce Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yi kokarin sulhunta Ganduje da Shekarau sai dai hakan bai samu ba.

Shekarau da Kwankwaso sun hade a NNPP

Za a iya cewa kurunkus domin a ranar Laraba, Jagoran G7 Sanata Ibrahim Shekarau ya fice daga Jam’iyyar APC tare da komawa Jam’iyyar NNPP, jam’iyyar da tsohon abokin hamayyarsa Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso ke jagoranta.

Abin jira a gani shi ne yadda za ta ci gaba da kayawa a siyasar ta Kano wadda ake wa take da sai dan Kano.