✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda karyewar gada ta kashe mutum 18 a Kano

Magidanci da iyalansa sun rasu a hanyar kai wa ’yarsa ziyara a makaranta.

Karyewar gada ta yi ajalin matafiya 18 ciki har da wani magidanci da iyalansa mutum biyar a kan hanyar Riruwa zuwa Doguwa a Jihar Kano.

Malam Bashir Doguwa da iyalan nasa da ke kan hanyarsu ta kai wa ’yarsu da ke rubuta jarabawar kammala sakandare ziyara a makarantar kwana, tare da sauran fasinjojin sun rasu ne bayan motar ta fada a ruwa sakamakon karyewar Gadar Shuburu.

Matafiyan sun gamu da ajalinsu ne a lokacin da ake tafka ruwan sama kamar da bakin kwarya a kan hanyar da ake yawan bi.

Wasu direbobi sun ce hanyar ba ta nuna alamar hatsari ba, musamman a kusa da gadar ta Shuburu, amma Aminiya ta gano cewa gadar tana cikin mummunan yanayi, har zuwa ranar Juma’a 23 ga watan Yuli da ta rufta ta kuma kashe mutum 18 din.

Shaidu sun tabbatar mana cewa ana ruwan sama sosai lokacin da matafiyan su 18 a cikin wata mota kirar VolksWagen Sharon suka bar Doguwa.

Ganau sun ce hatsarin da ya ritsa da daukacin matafiyan ya faru ne sakamakon ruftawar da gadar ta yi saboda tsananin karfin ruwan sama.

‘Rashin sani ne’

A cewarsu, a lokacin da motar ta zo wurin da gudu, direban bai san da karyewar gadar ba, don haka ta fada cikin ruwan ta kashe duk mutum 18 da ke cikinta.

Wani wanda ya ga abin da ya faru ya shaida mana cewa da a lokacin da motar ta zo direban ya san halin da gadar take ciki da hakan ba ta faru ba.

A cewarsa, duk da cewa gadar ba ta nuna alamun lalacewa ba, mutanen kauyen da ke kusa da ita sun san cewa tana matukar bukatar gyara.

Wani sashe na gadar ta ta karye. (Hoto: Ibrahim Musa Giginyu).

Wani mazaunin Doguwa, Malam Shehu Bello, ya bayyana cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 8:00 na dare, shi ya sa duhu da ruwan sama za su hana direban ganin hanya da kyau.

Ya ce a cikin daren mutane nagari suka fito aka yi ta nemo wadanda abin ya rutsa da su, kuma an gano gawarwakin mutum 15 a wurare daban-daban a gabar ruwa, washegari da safe kuma aka gano sauran.

Abin gwanin ban tausayi

Ya ce an yi amfani da alamun shaida a aka gano a wurin wadanda abin ya rutsa da su aka tuntubi danginsu kuma zuwa safiya galibinsu sun zo don gano ’yan uwansu da abin ya rutsa da su.

“Abun gwanin ban tausayi lokacin da iyalan yawancin mamatan suka zo da safe don neman danginsu da suka rasu; abin takaici ne kuma muna rokon Allah Ya ba su hakurin jure rashin,” inji Malam Bello.

Shi ma Malam Sani Ubale, daga cikin shaidun, ya ce lokacin da matafiyan suka zo inda gadar ta rushe, direban ya yi iya kokarinsa wajen kawar da motar amma lokaci ya riga ya kure masa, sai motar ta fada cikin ruwan, wanda hakan ya yi sanadiyyar nutsewar fasinjojin.

Magidanci da iyalansa

Malam Sani ya kara bayyana cewa mutum shida daga cikin wadanda hatsarin ya rutsa da su ’yan gida daya ne da ke kan hanyarsu ta kai wa ’yarsu da ke rubuta jarabwar kammala sakandare a makarantar kwana ziyara.

Malam Bashir Doguwa, mahaifin Firdausi Bashir, dalibar ajin karshe a  Makarantar Sakandaren Kimiyya ta First Lady, ya rasa ransa a hadarin tare da wasu mutum biyar ’yan gidansa.

Sanarwar da Ma’aikatar Ilimi ta jihar ta fitar ta bayyana cewa Malam Bashir da iyalan nasa suna kan hanyarsu daga Doguwa zuwa Makarantar Sakandaren Uwargidan Shugaban Kasa don ziyartar ’yarsa Firdausi da ke cikin daliban makarantar masu rubuta jarabawar NECO da ke gudana.

An yi babban rashi —Ma’aikatar Ilimi

A sakonsa na ta’aziyya, Kwamishinan Ilimi na Jihar Kano, Muhammad Sanusi Sa’id Kiru, ya bayyana lamarin “a matsayin babban rashi ga mutanen Karamar Hukumar Doguwa da ma jihar baki daya”.

Kwamandan Hukumar Kiyaye Haddura ta Kasa (FRSC) a Jihar Kano, Zubairu Mato, ya yi bayanin cewa hatsarin ya faru ne lokacin da gadar da ta hada Riruwai da Doguwa ta karye sakamakon ruwan sama mai karfi.

Ya bayyana cewa mamatan sun hada da yara bakwai da manya 11.

A lokacin da aka tuntube shi, Babban Sakataren Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar (SEMA), Saleh Jili, ya tabbatar da faruwar lamarin wanda ya ce abin takaici ne.

Ya kuma bayyana cewa tuni Hukumar ta tura wakilai don jajantawa ga iyalan wadanda abin ya shafa.

Jami’in ya kara da cewa gwamnatin jihar tana tantance halin da ake ciki don magance matsalolin da suka taso dangane da rushewar gadar da sauran kalubalen.

Tuni dai aka binne gawarwakin kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.