✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda hatsarin tankar mai ya lakume rayuka a Zariya

An yi hatsarin ne a Gadar Dan Magaji da ke Wusasa, Zariya da misalin karfe shida na safiyar Alhamis

Wani mummunar hatsarin tankan mai ya lakume rayukan mutum uku da dukiyar miliyoyin Naira a kan babbar hanyar Kaduna zuwa Kano.

Wannan hatsarin tankar mai ya auku ne a Gadar Dan Magaji da ke Wusasa, Zariya, da misalin karfe shida na safiyar Alhamis, kamar yadda Kwamandan Hukumar Kiyaye Haddura ta Kasa (FRSC) Reshen Zariya, Abdurrahaman Yakasai, ya shaida wa Aminiya.

Mataimakin Shugaban Kungiyar Dillalan Man Fetur na Kasa (IPMAN) Reshen Jihar Kaduna, Maiwada Zariya, ya ce motar mai lamba RNG 065 XA (Jigawa) ta taso ne daga Legas zuwa Kano dauke da litar mai kusan Dubu arba’in da biyar.

Ya ce hatsarin ya aukune bayan direban tanakar man ya kauce wa wani direban motar bas mai tukin ganganci da ya dauko kaji, a garin kaucewa nauyin tankar ya rinjaye ta, ta fadi, ta kama da wuta.

Zuwa lokacin da wakilinmu ya zanta da shi, ya ce, ba a kai ga gano mutanen da hatsarin ya rutsa da su ba, amma an kai gawarwakinsu Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Shika, Zariya.

Maiwada Zariya ya bayyana cewar tanakar ba ta danne kowa ba kamar yadda ake yada jita-jita cewa ta danne wadansu almajirau masu wucewa.

Ya ce, “Yazu haka mun sami nasarar daga takar kuma babu kowa a karkashinta, sai dai wutar motar ta kona shaguna da ke kusa da wurin kuma a lokacin masu shi ba su isa budewa ba.”