✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda Dalibi ke kokarin mayar da gashin kaji ya zama abinci

Wani dalibi dan kasar Thailand mai suna Sorawut Kittibanthorn da ke zaune a Lardin Bangkok/Nakhon Pathom, ya fara bincike kan yadda za a sarrafa gashin…

Wani dalibi dan kasar Thailand mai suna Sorawut Kittibanthorn da ke zaune a Lardin Bangkok/Nakhon Pathom, ya fara bincike kan yadda za a sarrafa gashin fuka-fukan kajin da aka yanka domin mayar da su abinci, inda ya fara tattara tulin gashin fuka-fukan da ake zubarwa a kowace shekara.

Sorawut mai shekara 30, yana neman tallafin kudin da za su taimaka masa wajen yin wannan binciken kan yadda za a iya sauya gashin fuka- fukan kaji a nika su koma gari, sannan a sarrafa su su koma sanadarin da za a iya hada abinci mai dandano da dadin ci.

“Fuka-fukan kaji na dauke da sinadari mai gina jiki, idan za a iya sauya fuka-fukan zuwa wani nau’in abinci da za a iya fitar da shi zuwa wasu kasashen waje, hakan zai sa a rage watsar da gashin fuka-fukan a juji,” a cewar Sorawut yayin zantawarsa da Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters.

Wannan babban bincike ne, wanda ya sa Sorawut ya tanadi tan miliyan 2.3 na gashin fuka- fukan kajin da ake zubarwa a kasashen Turai a kowace shekara.

Tsarin binciken ya nuna cewa za a iya amfani da gashin fuka-fukan wajen yin wani abinci, sannan an samu sakamako mai ma’ana bayan yin wani bincike.

Wani mai kula da shafukan sadarwar Intanet kan abinci mai suna Cholrapee Asbinbichit ya ce, “Ka san gashin kaji yana da wani yanayi da tarin abubuwa, da za a iya hada su da dankalin Turawa da salad inda zai iya zama wani abinci na musamman.

“Bayan tattara fuka-fukan ya zama kamar wani tsokar nama, tare da sauya shi ya zama wani sinadari da za a iya amfani da shi a wajen girki, zan yi matukar murna idan zan same shi a gidan abinci.”

Wani Farfesan kimiyyar abinci mai suna Hathairat Rimkeeree da ke Jami’ar Kasesart, ya yi mamakin sakamakon binciken.

“Ina tunanin hakan zai yi kyau kuma zai iya zama wani zabin abinci ko hanyar samar da abinci a nan gaba,” inji Hathairat.

Hanyoyin dabarun musayar cin nama zuwa cin abincin da ke da ganyayyaki na ci gaba da samun karbuwa ga jama’a da yawa.

Kuma a kan kauce wa fargabar cin naman dabbobi da wasu cututtuka na muhalli da ka iya shafar dabbobin da ake kiwo a gonaki.

“Tunda ba a iya tsara abincin da aka yi daga fuka- fukan kaji ba, zai yi kyau ya zama cikin jerin abinci da mutum zai iya zaba don gamsarwa,”inji Sorawut.

Sorawut ya kara da cewa, “Ina shirin samar da gidajen abincin da ba a iya zubar da abubuwan da aka fitar na amfani don yin abincin, duk da yake wannan abincin an samar da shi ne daga abubuwan da ake zubarwa a juji daga dabbobin da ake ci.”